CALENDAR METHOD OF FAMILY PLANNING
Mutane da yawa sukan yi tambaya akan ta
Yaya za a samu hanya Mafi sauki ta yin
tazarar haihuwa, ba tareda shan kwayoyin
contraceptives ba, duba da yadda Yawancin su
sunada yawan side effects, to ga bayanin a
bayyane!
WANNAN AMSA TA KUNSHI:-
1-Dalilin da ke jawowa 'yan mata yawan ciwon
ciki ko ciwon mara musamman bayan Haila.
2-Yanda ma'aurata zasu yi 'family planning' ba
tareda shan magani ba.
3-Abinda ke fitowa wasu mata mai kamar
majina, da sauransu.
Da farko, zan yi amfani da kalmomin hausa
domin samun sauqin fahimta, kalmomin
turancin da ban san ma'anar su da hausa ba
don haka zanyi kwatancen da za'a gane!
Idan nazo kan FAMILY PLANNING zan yi
bayani akan abinda bincike ya tabbatar, amma
ba sai na maimaita ba, Allah Ya kan iya canja ikon sa koda anyi hakan kuma a samu
haihuwa, amma Insha Allah ba'a cika samun
haihuwa ba idan akayi hakan.
Da farko,A jikin mahaifar mace, (Uterus in
female reproductive system) idan muka lura,
zamu ga wasu abubuwa kamar hannaye guda
biyu, daya gefen dama dayan kuma gefen
hagu, a bakin ko wanne akwai wani abu
qullutu wanda a cikin sa akwai wasu kwayaye.
Duk sanda Mace tayi Jinin ta na Haila bayan
jinin ya dauke da kwanaki 14,wancan abu
dana ambata yana sakin wadancan kwayayen
(eggs) wadanda sune sinadarin da ake
hadawa a samu da'.
Wadannan kwayaye idan aka sake su sukan
shiga cikin mahaifar mace suyi kwanaki 2
(48hours) daga nan idan babu abinda yazo ya
ta6asu, wato na daga sperm(maniyin Namiji)
to zasu mutu.
Kafin a saki wadannan kwayayen akwai abinda
Allah Ya halitta a cikin mahaifar mace wanda
zai zo ya share mahaifar ta sosai, domin
mahaifar zatayi baqo(stranger), wanda shine
wannan kwan kenan. Sannan,Akwai wasu
jijiyoyi guda biyu na jini, a gefen dama da
hagu na mahaifar mace, idan akazo aka share
mahaifar, to wadannan jijiyoyin zasu cika da
jini sosai, saisu koma ja-ja- wur, suna jiran
wannan baqon da zai shigo mahaifa idan ya
girma bai mutu ba sai su rika bashi wannan
jinin a matsayin abinci.
Shi kuma maniyyin 'da Namiji yana yin
kwanaki 3(72hours) a cikin mahaifar mace
kafin ya mutu, sa6anin na mace dake kwana 2
(48hrs).
!
!
!
!
!
Idan mun fahimci wadancan bayanan da suka
gabata, to yanzu sai mu hada su waje daya
muga yadda abin yake;
Idan Mace ta gama haila da kwanaki 14 to
wancan abun mai kamar tiyo (follopian tube)
na jikin mahaifar ta yakan saki wadannan
kwayayen, zasu shigo cikin mahaifarta suna
jiran Maniyyin Namiji yazo ya same su, idan
suka hadu komai qarancin Maniyyin nan, to
Maniyyin zai zamo musu kamar taki(fertilizer)
don haka zasu hadu su girma, da hakane
kuma Allah zai yita sarrafa shi cikin ikon da
buwayarsa har ya maida shi mutum!
SUBHANALLAH!!
To idan kuwa babu wani Maniyyi da ya shigo
wurin a dalilin rashin saduwa da macen, to
wadannan kwayayen zasu mutu bayan sunyi
awa 48 (kwanaki 2), idan kuma suka mutu to
zasu biyo cikin al'aurar mace sai su fito, sai
kaji mata na tambayar sukan ga wani abu mai
kamar majina-majina yana fito musu a al'aura,
wannan shine abinda ke fitowar! Wannan ya
sa malamai suka ce babu komai akan wannan
kawai ta wanke shi ba shida wani hukunci.
In the same boat;
A dalilin rashin shigar Maniyyi da zai girmar
da wancan kwan, sai wadancan jijiyoyi da
suka tara jini a cikinsu, sai suyi wani abu da
ake kira fushi,(wataubasu ji dadi ba)adalilin
haka sai su rinka kartar jikin mahaifar mace,
sai kaji mace tace maka tana yawan fama da
ciwon mara (lower abdominal pain)
musamman idan ta gama Haila.
Idan karce jijiyoyin nan yayi yawa kuma aka yi
rashin sa'a sai su fashe, idan kuma suka
fashe sai jini yayita fita ba tsayawa, wannan
shine ake qira da jinin Istihada, daman
Manzon Allah (s.a.w) ya taba gayawa wata
mata cewar ai wannan jinin na jijiya ne.
FAMILY PLANNING:-
Idan Matar aure ce kuma tana son yin family planning da Mijinta, to hanya mafi sauqi
itace;
Kamar yadda muka ji cewa bayan gama hailar
mace da kwanaki 14 ake sakin wadancan
kwayayen, kuma sukan yi kwanaki 2 kafin su
mutu, shi kuma maniyyin namijin yakan yi
kwanaki 3 kafin ya mutu, to su ma'auratan
kada su sadu tun ranar 12 da gama hailar ta,
har sai bayan ranar 16 da gama hailar ta.
Mu dan tsaya kadan anan kafin muci gaba
muyi tunanin meyasa akace haka?
Dalilin hakan kuwa shine,ranar 14 kwai ke
zuwa, to idan suka sadu ranar 12, kada mu
manta Maniyyi sai yayi kwanaki 3 kafin ya
mutu, to kunga idan suka sadu ranar 12,
maniyyin nan yananan a mahaifar yana jiran
ranar 14 a saki kwan, zai zauna na tsawon
kwanakin 12,13,14 kafin ya mutu, to kunga
zasu ci karo ranar 14, kuma babu abinda zai
hanashi sarrafa wannan kwan,saidai wani
hukunci na ubangiji!,har sai bayan ranar 16 ne
saboda shi kuma kwai yakan yi kwanaki 2
kafin ya mutu!
To wadannan kwanaki 5 din,watau
12,13,14,15 da 16 da gama Hailar mace, su
ake qira da DANGER PERIODS(kamar yadda
nataba fada
takaitaccen bayani kwanaki), ma'ana kwanaki
masu hatsari, an kira su da hakane saboda
idan dai aka sadu da Mace a wadannan
kwanakin to kuwa tabbas zata samu ciki, sai
dai idan Mulkin Ubangiji ya shigo ciki, kuma
idan ma'aurata na son yin family planningt, towadannan kwanakin
zasu kaucewa saduwa aciki, ba sai sun sha
magani ba, sai dai idan Mulkin Ubangiji ya
shigo ciki.
NOTE:-
Gameda danger period da akayi magana,akan
samu variation daga mace zuwa mace(Wajen
farawa da gama al'ada)for that,wannan zai
zama as a guideline ne kawai!
Bissalam
Sai mun hadu a wani post din.
Comments
Post a Comment