CIGABA DA DARASIN COMPUTER. AMFANIN KEYBOARD
Wancan darasin mun tsaya ne a kashe-kashen keyboard da muke dasu.
To a yau ma akwai wasu keyboard da ya kamata muyi bayani akansu saboda muhimmanci su.
Cikin wadan nan madannai akwai;
ENTER OR RETURN KEY; Wannan key kamar yadda sunan shi yake ' enter ana amfani da shi wajen shiga wani program ko software, sannan zaka iya double click to return back, wato ka fito normal place da kashi ga daga farko. Sannan ana amfani da enter key wajen typing for spacing.
TAB KEY; Ana amfani dashi ne for paragraph, sannan ana amfani dashi for navigation.
BACKSPACE KEY: ana amfani dashi wajen yin deleting din errors in ana typing
SHIFT KEY; Ana amfani da shift key wajen combination with other keys. Wato ana hada shift key da wani key din don samar da wani abin misali shiftkey + Letter A key = Capital A
CAPS LOCK KEY; Shi kum wannan ana amfani dashi ne wajen mayar da letter Capital, duk letter key da akai typing zata kasan ce in Capital har sai anyi turning dinsa off.
Bayan wannan keys kuma akwai mouse, mouse dashi akeyin duk wani abu a cikin computer, dasu ale controlling komai.
Mouse kala biyu ne, akwai na desktop, akwai na laptop.
Mouse na desktop daban yake yana zaman kanshi, shiko na laptop a jikin laptop din take daga sama kasan keyboards..
To dukkansu amfaninsu daya ne, kowane yana da buttons guda biyu left and right
LEFT BUTTON; idan akai clicking, ko ince danna left button anyi selecting item, in akai double click shine zai bude application ko window.
RIGHT BUTTON; idan akai clicking right button kan wani item to zai bude menu, dake da shortcut, sannan yana nuna options ga file ko program.
Ga wasu shortcut key system.
CTRL+A =. Select all/highlights all wato zaba gaba daya,
CTRL+C. =. Copy, kwafar rubutu, ko video ko hoto ko wani abu dai a clipboard sai ayi pasting a wani wajen.
CTRL+X. =. Cut, daukewa daga wani don canza mai wuri.
CTRL +V = Paste. Sauke abin da akayo copy ko cut.
CTRL+Z = Undo, misali kayi selecting wani abu ka goge shi mistakenly ko wani abin daban, to sai ayi cntrl z don undo din abin ya koma normal ydda yake.
CTRL+B = Bold, don mayar da rubutu yayi kauri, kamar heading sai ay masa ctrl b zai koma bold.
CTRL+U = Underline, don ja ma rubutu layi, sai ayi cntrl u
CTRL+I = Italic. Don mayar da rubutu zuwa italic styles, sai ayi cntrl I.
Mu hadu a darasi nagaba.
Comments
Post a Comment