DARENKA NA FARKO ACIKIN QABARINKA
'Dan uwa, duk abinda zaka karanta din nan babu tatsuniya ko kokwanto acikinsa. Zauren Fiqhu ya tattaro bayanin ne daga Sahihan Hadisai na Manzon Allah (saww) wadanda Manyan Malamai suka tattaro acikin litattafansu.
Darenka na farko acikin Qabarinka shine dare mafi razani da firgitarwa daga cikin dukkan darare..
Hakika tun lokacin da suka zo suka binneka, Idan sun ajiyeka agefen Qabarinka, Shi kansa Qabarin zai yi magana dakai. Zai tambayeka shin Mai kake gani acikinsa??
Zaka ce masa ai babu komai. Shi kuma zai ce maka, to duk abinda ka gani na alkhairi ko Sharri, to kaine kazo da abinka!!!
Idan kai mutumin banza ne mai bin son zuciyarsa, mai biyewa Sha'awarsa, To shaitan ya riga yasan ya gama dakai. Don haka zai zo gefen Qabarinka yana yi maka dariyar Mugunta..
Idan kuwa ka zamanto mutumin Kirki mai tsoron Allah, mai Halayen Kirki, To tun daga mutuwarka shaitan zai rika tsula kuka da eehu wai saboda bai samu damar dulmiyar dakai cikin hallaka ba.
Idan sun gama binneka, Allah zai dawo maka da ruhinka cikin jikinka. Nan take zaka rika jin maganganun 'Yan uwanka amma babu damar ka amsa musu. Kana jin takun takalminsu amma babu damar ka tashi ka bisu!!!
Idan kai Mumini ne cikakke, Nan take zaka ga wasu Mala'iku farare masu kyawawan kamanni zasu shigo har cikin Qabarinka. Zasu yi maka sallama sannan su zaunar dakai su tambayeka :
"WANENE UBANGIJINKA? MENENE ADDININKA? KUMA MAI ZAKA CE GAME DA ANNABI MUHAMMADU (SAWW) - Zasu nuna maka siffarsa"
Zaka basu cikakkiyar amsa: "Allah ne Ubangijina, Musulunci ne addinina. Kuma Annabi Muhammadu (saww) Shine Manzona nayi imani dashi. Shine ya isar min da sakon Ubangiji".
Nan take Mala'ikun zasuyi maka kyawawan kalamai. Za'a nuna maka gidanka na Aljannah kuma za'a bude maka wata Kofa wacce ta nan ne ni'imomin cikinta zasu rika shigo maka har zuwa ranar tashin Alqiyamah.
Idan kuma Kafiri ne ko Munafiki (Mai imani abaki, amma zuciyarsa babu Soyayyar Ma'aiki saww) Ko kuma mai bin son zuciyarsa, awannan lokacin zai ga wasu Mala'iku Baqaqe Wuluk masu mummunar kamanni..
Zasu shigo har cikin Qabarinsa, su tasheshi su zaunar dashi Sannan su tambayeshi "WANENE UBANGIJINKA, MENENE ADDININKA, KUMA MAI ZAKA CE DANGANE DA ANNABI MUHAMMADU (SAWW)"
Zai ce "Aah!! Aah!! Ban sani ba! Ban sani ba!!" Sai Mala'iku su fara Jibgarsa da wata irin gudumar Baqin Qarfe wacce ba zata misaltu ba.. Idan ya kwarara Eehu sai dukkan halittu sunji shi. in banda mutane da Aljanu!!!
'Wannan ranar tana nan zuwa garemu baki daya. Dani dakai, Dake, daku, duk Sai mutuwa ta riskemu.. Kuma sai munyi kwanciyar Qabari.. Kuma sai an tambayemu akan ayyukanmu..
Shin sau nawa kake tuna wannan ranar a kullum?? Shin kana yin tanadi domin zuwanta?? Ko kuma tanadin gyaran duniyarka kawai kakeyi??
Ni dai na duba cikin ayyukana ban ga wani abinda zan doshi Allah dashi ba.. Sai dai Son Allah da Manzonsa (saww).
Ya Allah afuwarka nake kwadayi.. Rahamarka nake roko, Falalarka nake sa rai.. Ya Allah ka gafarta mana ka gafarta ma Iyayenmu da Malumanmu da iyalanmu da dukkan Musulmai maza da mata.
Tunasarwa ce daga ZAUREN FIQHU da fatan duk wanda ya samu zai tura ma 'Yan uwa Musulmai ba tare da Editing ko chanza wani abu daga cikin sakon nan ba.
KA TUNA DA DAREN FARKO ACIKIN QABARINKA!!!
MAGANAN MAGABATAN KWARAI
.
IBNUL- QAYYIM (RM) YACE
Babu Wani Mutum da Zai Wadatu dasu (Falaqi Da Nãss) Kuma Lallai Suna da Wani Ta'asĩri Kebabbe Cikin Bada Kãriya ga (Sihiri,) da (Kambun baka) da Sauran (Sharrori).
Kuma Lallai Buqatuwar Bãwa ga Neman Tsari da Wadannan Surorin Guda Biyu (Falaqi Da Nãss) Sunfi Girman Buqatuwar Sa ga (Numfashi) da (Abinci) da (Abin Sha) da (Tufafi)
[ بدائع الفوائد (١٩٩/٢) ]
.
MALAM YA KARA DA CEWA:
Hakika Wadannan Surorin Guda Biyu ( Falaqi Da Nãss ) Sun Tattare Neman Tsari ga Dukka Sharri, Kuma Suna da Wani Sha'ani Mai Girma Cikin Bada Tsaro da Garkuwa, daga Sharrori Kafin Afkuwar Su,
Sabo da Hakane Ma Manzon Allah (saw) Yayi Wasiyya ga Sahabinsa Mai Suna ( Uqbatu bin Ãmirr ) da Karanta Su Abayan Kowace Sallah
[ زاد المعاد (165/4)
KUYI SALATI A GARESHI ﷺ
Mai yin salati a gareshi yana amsa kira/gayyatar da Allah Yayi ne ga Muminai da suyi salati a gareshi acikin suratul Ahzab.
یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَیۡهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسۡلِیمًا
Mai yin salati a gareshi yana muwafaqa ne da Allah da mala'ikunSa (Wato yana yin irin abinda suke yi) saboda fadin sa Madaukakin sarki;
إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَـٰۤىِٕكَتَهُۥ یُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِیِّۚ
Mai yawaita salati a gareshi yana riqo ne wani sababi da zai gadar masa da samun kusanci da cetonsa a ranar alkiyama.
Sheik Uthaimin (rahimahulLah) yana cewa:
"Ban ta6a sanin wani wanda yake son Allah da ManzonSa ba, da zai iya barin yin salati ga Manzon Allah (ﷺ).
[لقاء الباب المفتوح ٢٣٤]
Abu Hamid al sa'adi (Allah Ya yarda dashi) yace;
"(Mu sahabbai muka ce); ya Manzon Allah! Yaya zamuyi salati a gareka?"
Sai (Manzon Allah ﷺ) yace;
اللهم صل على محمد و على ال محمد، كما صليت على إبراهيم و على ال إبراهيم إنك حميد مجيد، اللهم بارك على محمد و على ال محمد كما باركت على إبراهيم و على ال إبراهيم إنك حميد مجيد.
"ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD KAMA SALLAITA ALA IBRAHIM WA ALA ALI IBRAHIM INNAKA HAMEEDUN MAJEED. ALLAHUMMA BARIK ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD KAMA BARAKTA ALA IBRAHIM WA ALA ALI IBRAHIM INNAKA HAMIDUN MAJEED."
[Bukhari da Muslim]
DAREN JUMU'A/RANAR JUMU'A
Kar a manta da yawaita salati a gareshi SWA
TSARABA DAGA TASKAR GIDAN MANZON ALLAH ﷺ
Darasi na farko-(1)
Mafi cikar abin koyi ga al'umma shine Manzon Allah ﷺ acikin dukkan rayuwa baki daya,mutum yana samun shiriyane gwargwadon yanda yayi koyi da Manzon Allah ﷺ acikin dukkan al'amarinsa na rayuwa.
Wannan darasi zai fassara wasu hadisai ne wadanda aka ruwaito su game da yanda Manzon Allah ﷺ ya zauna da iyalinsa a rayuwar aure dan muyi koyin haka muma acikin rayuwar auren mu dan cewa da koyi da shiriyar Manzon Allah ﷺ.
*1-Cin abinci tare,tare da sanya baki a inda miji ko mata yaci dan nuna soyayya da kauna*
Daga Nana A'isha R.A tana cewa;-
*"Na kasance ina shan abin sha alhali ina lokacin Haila sannan na miqawa Manzon Allah ﷺ abin shan sai ya sanya bakinsa inda na sanya nawa shima yasha,kuma na kasance ina lokacin Haila sai na dauki kashi na gutsira sannan na miqawa Manzon Allah ﷺ shima sai ya sanya bakinsa a daidai inda na sanya bakina sai shima ya ci daga nan"*
@صحيح مسلم.
Zamu dauki darasi a wannan hadisi mai girma kamar haka;-
-Manzon Allah ﷺ shine mafi alkhairin mai gida,saboda yafi kowa alkhairi wajan iyalinsa.
-Yanda Manzon Allah yake nunawa iyalinsa so da kauna dan ya kwantar masu da hankali da nuna masu tausayi da jin kai.
-Halascin ci abinci da abinsha da mai Haila da kuma nuna cewa mai haila ba najasa bace ba sannan ya halasta kayi mu'amala da mai haila sabin Yahuda da suka haramta hakan.
-Saukin hali na Manzon Allah ﷺ da yin dukkan abinda zai kwantar da hankalin iyalinsa tare da nuna mata love.
-Sunnah shine mata da miji suci abinda tare saboda hakan yana kara masu so da kauna shaquwa da juna.
-Sannan hadisin ya nuna sauran abinci bakin mutum ba haramunn bane ba sannan hadisin ya kara koyar da mu akan wajibine ga uwar gida da mai gida suriqa kulawa da jikinsu musamman bakinsu saboda ibadar aure.
Kadan kenan daga abinda muka fahimta a wannan Hadisin mai girma.
Allah ne mafi sani.
*Rayuwa mai dadi tana tare da koyi da Manzon Allah ﷺ acikin dukkan komai*.
Mu hadu a darasi na gaba insha Allah.
Comments
Post a Comment