Main menu

Pages

ANYOYIN DOREWAR ZAMANTAKEWAR MA'AURATAN DA BA SU ZAUNE A WURI DAYA


Lalle ko shakka babu, zamantakewar ma’aurata ko saurayi da budurwar da za su yi aure amman ba sa zaune wuri daya na da wahala.


Sai an hada da dauriya da hakuri. Wani abu kuma, bai kamata su bari wannan tazarar ta yi sanadiyar zaman su ba.


Wadansu mazajen kan bar matansu su tafi zuwa wani gari saboda dalilin aiki, kasuwanci, karatu ko wani abu daban. 


A irin wannan yanayin, akwai abubuwan da ya dace da ma’auratan ko samarin don gudun fadawa matsala. Ga wasu daga cikin su.


Tuntubar Juna:


Tuntubar juna, wato yin wayar salula na taimakawa a irin wannan yanayin. To sai dai, dayawan mutanen ba su fahimci ainafin abunda a ke nufi da hakan ba. 


Yin waya ba yana nufin a yi ta waya ne koyaushe ba, a’a, ya danganta dai.


Da ma amfanin zama tare shi ne domin kara kusantar juna da shakuwa, to a irin wannan yanayin, sai ku tsara yanda za ku yi na ganin cewa kun cike wancan gibin bisa abunda ku ka amince da shi a tsakanin ku.


Nisa ya na kara sa so da kauna, zuciya kuwa na son kulawa. To sai dai, ta bakin malam bahaushe: “mutum dan tara ne bai cika goma ba.


” dole sai an hada da yi wa juna uzuri da kyakkyawan zato, ba lalle ba ne ta/ya iya yin waya watarana ba kamar yanda aka saba,


 saboda haka kar wannan ya sanya ka/ki wani tunani maras kyau a kan abokin zaman ka/ki.


A Guji Zargi:


Gaskiyar magana, ba wani zaman aure ko soyayyar neman aure da za ta iya dorewa idan ba bu yarda a ciki. A cikin zamantakewar nesa kuwa, a nan ne ake tsananin bukatar yarda da kyautata zato ga abokin zaman ka/ki. 


Idan har ka/ki na da wani rashin natsuwa a zuci, to sai a hada da addu’a domin samun natsuwa. To amman dai, ko ta yaya ma ka yi kokarin koya wa kan ka/ki yarda da abokin zaman ka/ki.


Kar ka/ki zama mai fassara duk wani motsi ko aikin abokin zaman ka/ki, ta hanyar sama rai shin wai ko ya daina son ka/ki. 


Lalle hakan na haifar da matsala ga zamantakewa, yana kuma haifar da matsalar bugun zuciya da ma matsala a jiki.



Ziyarar Juna:

Idan an samu damar ziyarar juna, to yana da kyau a yi anfani da damar lokaci bayan lokaci bisa yanda ku ka tsara a tsakanin ku


Idan kuwa ba bu lokacin haduwar, to za ku iya sanya wani abu da za ku yi tare alhalin baku wuri daya don kara kulla dankon soyayya a cikin kwakwalwarku. Yin hakan zai rage matsalar kewa.


Kyautatawa:

Baya ga cewa nisa a zamantakewa na kara shakuwa da so, to kuma yana sa ‘yar karamar kyauta ta faranta ran masoyi/masoyiya yanda ba a zata ba. 


 Misali, tura sakon waya zai faranta rai da kara shaukin soyayya, haka kuma, aika ‘yar wata tsaraba ko da kai baka samu zuwa ba na da tasiri sosai a zuci. 


Saboda haka, za a iya anfani da nisan zamantakewa wurin kara dankon soyayya a maimakon fada, rashin jutuwa ko rabuwa.


Hanyoyin Yin Mu’amala Da Ma Su Nakasa

Shin ko ka na kallon da bai kamata ba ga mutane ma su nakasa, nuna kyama da wariya?


A cikin al’ummar da mu ke rayuwa, mu kan hadu da ma su nakasa a cikin ‘yan uwan mu ne, abokai, makaranta ko wurin aiki da sauran su dai. Wani makaho ne, gurgu, kurma, da dai sauran nau’in rashin lafiya (nakasa).


Wadannan wadansu hanyoyin yin mu’amala da ma su nakasa ne da za su iya taimaka mana a yayin hulda da su.


1. Ba da gudanmawar taimako: Mutum ya kan nemi taimako ne a halin da ya zama shi ba zai iya yi wa kansa ba. Alal misali, tsallakar da makaho kan hanya, taimako ne da zai ji dadin sa.


2. Girmama Su: Ya kamata ne a girmama mutane ma su nakasa kamar yanda za a girmama kowa. Kar ai ma su wani kallo daban sabanin irin wanda a ke wa sauran mutane. 


Sannan wani abu, idan har za a yi wa mai nakasa wani suna na lakabi, to ya kamata ne a kira shi da sunan da ba zai ji damuwa ba; a ji ta bakinsa idan ko da wani lakabin da shi yafi so. Kamar dai yanda a ke cewa, kar ka yi wa wani abunda kai ba za ka so a yi maka ba.


3. Yin magana kai tsaye zuwa gare shi: Akwai ciwo da damuwa sosai ga mai nakasa ya zama cewa, yayin da wani ke son yin magana da shi ba zai yi da shi ba, sai dai wai da dan-jagoransa. 


Haka kuma, idan za ka yi magana da wanda ke kan keken guragu, to ka yi magana da shi ne kai tsaye a maimakon mai tura sa.


4. Sanya Fata Gare Su: A duk lokacin da ka hadu da mai nakasa, to ka yi kokarin karfafasu da basu magana ta hanyar kalamanka.


 Yi kokarin ba su shawarwari kan abunda zai taimaki halin da su ke ciki


5. Bayar Da Taimako Gare Su: Wasu mutanen kan ji tsoron taimaka wa ma su nakasa ko don tsoron kar su (ma su nakasar) su ji wani abu a ran su. Abunda ya kamata shi ne, yayin da za ka taimaka ma su kan yin wani abu misali, to kar ka yi kana mai yin mummunan duba, nuna kyama ko wani abu makamaicin wannan a gare su.



Comments