"GANI GA WANE, YA ISHE WANE TSORON ALLAH" Jan Hankali ga Matan Aure Ku yi Hattara Ku Kiyaye...
A TRUE LIFE STORY
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai wan nan labari yafaru ne da gaske da fatan zamu kiyaye da duk abinda wannan dan guntun labarin zai Karantar.Allah Yasa mu dace Ameen Mai wannan labarin ta boye sunan garinsu saboda gudun magana.
" Sunana Hafsat, amma a k'auyenmu ana kira na Hafsee shekaru Na 24
Mahaifinah, headmaster k'auyen mu ne, Mahaifiyata ita kadaice matarsa , mu shidda ne a gurin Iyayenmu, maza 5 Sai kuma ni kadai mace,
Tun ina ss 1 abokin yayanah ya nuna yana sona, a lokacin yana A.B.U Zaria yana karatu, iyayena suka bashi damar magana da ni, amma dana kai karshen ss 2 sai maza suka yi caa akaina kowa na sona da aure.
Kasan cewa ni wankan tarwadace ce , dogowa ga gashi kai wasu ma suna mini kirari da *African beauty queen* Lol..
Amma duk wannan bai taba yaudara ta ba tunda nayi ma *Yusufa* alkawari ban kara kula kowa ba,
Ko samari sunzo gidan mu zance wuri na bana fita, har ya kai Mahaifina ya fara fita da kanshi Yana gayawa duk wanda ya zo wuri na anyi mini miji.
A kwana a tashi na gama secondary lokacin Yusufa yana NYSC a Kaduna, ni kuma da saka makon SSCE na ya fito na ci sosai duk da ina kaunar Yusufa ina da burin karatun aikin asibiti (ko likitanci ko nurse) domin in samu in taimaki yan uwana mata a fannin haihuwa,
Amma kash.....!
Mahaifina ya k'i, ya ce Yana tsoron bari na zuwa garin da ba dangi karatu kada mazan zamanin nan su yaudare ni.
Haka na hakura nayi zaman jiran Yusufa har ya gama NYSC ya samu aiki a Secondary School a Kaduna a kayi biki muka tare Kaduna da zama.
Gidan haya ya kama daki 2 da falo, cikin gidan apartment 4 ne, duk cikin matan babu wacce ta wuce shakaru 25 munyi zaman ammana da hadin kai, kasancewa nice ka dai mace a gidanmu, sai na dauke su tamkar yan uwa. A Kwana a tashi na samu ciki na haifi Faisal,
Yanada wata 6 nasake samu wani Cikin....nayi kuka Sosai amma sai Yusufa yayi ta bani hakuri,Ya nuna mini Haihuwa ai Arzikice kuma shiyanason yara.
Haka na hakura har cikin ya girma na fara zuwa asibiti awo. A lokacin Yusufa ya samu aiki da CBN, kuma muka yi sa'a aka ajiye shi a office dinsu na Kaduna bayan training da suka yi a Lagos.
Yusufa yayi mini alkawari Idan na haifu lafiya zan rubuta JAMB don ci gaba da karatuna.
Ammah kuma sai dai kash...???
Na haifu lafiya, na kuma rubuta JAMB na ci 231 kasan cewa Yusufa Yana koya mini kuma ya samo mani lesson teacher Wanda yake koyamin abubuwa da dama .
_Alhamdullah nasamu admission Bsc nursing_
"Zamu fara registration Sadiq yafara rashin lafiya, abun yaki ci yaki cinyewa , muka je asibitin a kayi duk Wani binciken da Za'ayi daga karshe dai sai a ka gano Sadiq Yana dauke da kwayar cutar *HIV*😳
" Likitta na fadin haka na daga kai na kalli Yusufa nace abun da ka dauko mana a wajen training din Kenan ko....??? ka cuce ni Yusufa Ka cutar da yaron da baisan komai ba Zuciya ta ta rufe na fara gani Biyu2 Faduwa nayi Kasa sumammiyya.
"Bayan wani lokaci na. Farfado sai naga Yusufa na zaune akan kujera a gefe na Yana kuka, nace munafuki kukan me zaka yi , bayan ka cuce ni, Yusufa yace wallahi sweetie na rantse miki da Allah ban kula ko wacce mace ba, ba ma a lagos ba tun ranar da son ki ya shiga raina har zuwa yau da kika kasance uwar 'ya'yana .
Na ce rufe mini baki, ka samu bindiga kawai ka zo ka karasa ni. Yusufa yayi shiru daman can ba me yawan magana bane.
Bayan Kwana biyu a ka sallame mu daga asibiti, bana ma Yusufa magana, ranar Monday da ya tafi office na tattara Kaya na, da yara na, na tafi kauye. Iyayena suka yi mamaki gani a gida ba tare da Yusufa ba, da na huta Mahaifiyata ta bukaci jin Abinda yakawoni dan tasan wannan Zuwan ba Lafiy ba... Ban b'oye komai ba na labarta mata tun Farkon Rashin Lafiyar Sadeeq har yanzu zuwana gida.
Bayan Mahaifina yadawo gida aka Sanar dashi Dalilin zuwana gida bai dauki Zafi ba hasalima Yasaka aka kirani Tambayar Farko daya yi mini itace Tare da Yusufa Akayi muku gwaji...?? nace A'a Sadeeq ne kawai akayi ma Yace na koma Zai kira Yusufa yaji daga gareshi.
Karfe 8 na dare mahaifina ya dau waya ya kira Yusufa yace mishi idan ba zai damu ba gobe da shi da ni da yaran zamu je Kaduna Domin Muje asibiti ayi mana Gwaji gaba ki Dayanmu, Yusufa yace toh Baba,
Amma yanzu haka Ina hanyar zuwa domin naje gida ban ga Hafsa ba na San Tayi yaji ne, shi yasa na biyo ta, nan da mintuna 20 zan iso gari Babana yace Allah yakawo ka lafiya ya ce amin kamin ya ajiye wayar.
Isorwar Yusufa keda wuya Babana ya tambayi Yusufa me ya faruwa tsakani na dashi Yusufa ya maimaita mishi labarin kamar yanda na fadawa babana, Bayan yagama ne ya shigo ya gaida ummatah!!!
Babana yace mini ki shirya gobe da safe zamu je Kaduna asibiti da maigidan ki domin ayi muku gwaji toh na amsa Banma bi takan Yusufa ba.
Washe gari kuwa tunda safe na tashi na shirya nida yara muka kama hanyar kaduna har Babana ma a Motar Yusufa da isar mu bamu tsaya ko ina ba sai Asibiti Bayan mungana da likita aka debi jinina dana Yara da kuma na Yusufa.
_30mns_
A ka fito da Result Sai dai abin mamaki nawa dana Sadeeq Positive na Yusufa da Faisal kuwa Negative. Ina ganin haka nace. How comes..?? Ni sam ban yarda ba.
Sai dai In Yusufa ya hada baki da likita ne dan ace shi bayada ita. To amma abin mamaki harda Faisal ma baya da ita sai ni kawai da Sadeeq...??
Mahaifina Da likita da Yusufa suka yi mini duk bayani amma ban yarda ba.
Daga karshe suka ce in fadi wani asibiti muje, haka muka je wanni asibiti sakamako ya nuna ni da dana Sadiq muna dauke da *HIV* Yusufa da Faisal kuma Basuda Komai.
Nan fa na yarda nafara kuka ina rantsuwa ban San komai akan wanna cutar ba kuma ban taba ko maganar soyyaya da wani ba da nake budurwa har zuwa aure na"
Yusufa yace yi hakuri Hafsa ni na cancanta in bada wanna shaidar a kanki. Ni nafi zargin asibitin da kika haifu, Yusufa ya ci gaba da cewa tun lokacin da aka ce sadiq na dauke da *HIV* na san akwai wani abu a boye da ba mu sani ba amma kin ki bani lokaci muyi shawara.
"Yanzu lawyer zan dauka Zanyi karan asibiti da kika haifu.
Yusufa dai yayi Karan asibitin, maganganu yafara yawa a unguwa matan da muke zaman haya suka juya mini baya basu kula ni, zaman Kaduna ya gagare ni dole na koma k'auye da zama.
5 Month da Yusufa ya kai kara aka Kore kara sabida rashin kwajkwaran shedu daga bangaren mu. Cikin matan da muke zaman haya gida daya dasu dayar ita ma ta je asibiti awo aka gano da ita da maigidanta suma suna dauke da kwayar cutar *HIV* , sauran mazajen gida suka kai matan su gwaji a ka gano dayar matan na dauke da cutar *HIV* amma mijin da yaran duk babu.
Abun dai ya zama abun mamaki da ban tsoro, mata Hudu a gidan haya da mazan su na dauke da *HIV* a lokaci guda, ko meye dalilin..........?
Ckin mazajen wasu na zargin matansu matan ma haka, har ya kai dayan ya saki matarsa kasancewar bashi da shi a lokacin gwajin. Bayan kwanaki wani likita a unguwan ya bawa mazajen mu shawara da a tara mu a bincike mu,Wata k'ila akwai wani abu da muka sani dangane da wan nan lalurar.
Yusufa ya zo k'auye ya dauko ni, daman tun a lokacin na ki zaman Kaduna nace ya sake ni kawai tunda shi bashi da cutar amma ya ki. Da muka iso aka fara binciken mu dukkan mu fadi wani abu da muke saya ko sha da dai sauransu Binciken dai yanuna cewa duk kanmu Muna yawan, *AMFANI DA MAGANIN MATA*
Wata Hajiya Haleema da mijinta ya rasu a abuja shekaru 4 da suka wuce itace me kawo mana mu saya.
Haka aka kira ta aka tambaye ts ko tana da masaniya akan halin da muke ciki kuma ina take samun maganin da take sayar mana, sai tace a kasuwa take saya wasu kuma tana hadawa da kanta.
Daga na suka ce ko zata taimaka a je asibiti da ita Domin ayi mata gwaji *HIV* Sam taki amincew ta fara ruwan Bala'in wai za'ayi mata sharri ne tace bazata ba abu kamar wasa saida a ka kaita police station,
yan sanda Sukasa akayi mata gwaji abin dai ba'acewa komai Har za'a turamu kotu, nan fa ta fara kuka tace mijinta ya mutu da *HIV* Shine ya lika mata Shine ta Kudiri niyar Itama saita Likawa wasu Sabida batajiba bata, ganiba aka Roro mata Bala'i .
Tace: akwai ranar da ta sayi maganin matan a kasuwa na ruwa wanda ake sawa a gaban mata, sai ta bude duk kwalba 20 da ta saya ta ringa diban ruwan gaban ta tana hada wa da magani sai ta rufe kwalban,
ranar ne ta zo gidan mu dama mun saba saya, tace mana ga sa maza tsalle, yafi duk Wanda muke saya kwau, #1000 each muka saya a lokacin ina dauke da ciki 7 months.
Duk muka saya mukayi amfani da shi cikin daren ranar washe gari muka gayawa junan mu munji dadi magani: Fatima ce kawai tace batayi amfani da shi ba saboda Bakonta dayazo cikin dare.
bayan kwana biyu mijin ta. Yana neman allura da zare zaiyi dinki ya gani, ya tambayi Fatima me zata yi da wannan sai tayi shiru ya dauka ya jefar yace daga yau idan kika sake yin amfani da wannan magunguna ban yafe ba,
daga lokacin Fatima bata sake saya ba kuma bata taba mana bayani ba sai yau Dalili da yasa Fatima ta tsira daga cutar *HIV* kenan Halima mai maganin mata ta ci gaba da cewa ba ta San yawan mata da ta sayar wa maganin ba.
In takaita muku labarin rayuwata, yanzu shekaru biyu da faruwan haka, Halima ta rasu, Aisha matar da mijin ta ya sake ta ita ma ta rasu daga complications from cervical cancer, khadija kuma suna tare da mijin nata suna Shan magani. Sai dai kash..... 😰😰😰😰😰, ni mun rabu da Yusufa kasancewan shi bashi da cutar *HIV* bayan duk wannan shekarun .
"Yanzu haka na sake rubuta JAMB na samu 267 an bani MBBS 1, Yusufa Bawan Allah bai ajiyeni ba ya saya mini gida da mota da masu aiki, kuma duk wata Yana bani albashi domin kula da yaran da ni kaina, kuma yayi mini alkawari biyan kudin makaranta da text books ko wani shekara. Faisal dai Yana makaranta amma Sadiq gashi nan dai yau lafiya gobe ba lafiya, duk da maganin da muke sha.
*Maganin mata yazama silar rabuwata da mijinah Dakuma jin dadinah*
_END_
SHAWARATAH GAREKU
_Please my Dear Sisters. Dan Allah kusan Irin Maganin da Zakuyi amfani dashi Wallahi Koma ba wannan ba Akwai Cututtuka dayake coursing da dama irinsu. Cancer, Infection, Ciyon sanyi Dadai sauran Cututtuka Da Dama ,
kunga dai Abinda yafaru ga Malama Hafsat In kunne yaji jiki Ya Tsira kukan Kurciya Jawabi ne Mai Hankali yake Ganewa......._👉
Comments
Post a Comment