YADDA ZA A MAGANCE BUSHEWAR FATA.
Yadda za a gane cewa busasshiyar fata ne dake ta wadanan alamomin;
Saurin bushewar fata lokacin hunturu ko dari, yawan yin saba, kyasfi, fashewar lebe a lokacin iska ko dari, yawan jin kaikayi da kuma fata tayi fururu kamar an bada gari ko filawa.
Ya mutsewar fata da tayi tamoji tamoji kamar jikin tsohuwa, da sauran ire iren hakane.
Irin wannan fatar tafi kowacce fata bukatar gyara, sannan wannan darasin ya zo da hanyoyin magance matsalar bushewar fata.
Hanyoyin kuwa sune kamar haka;
- Ki daina wanka da ruwa mai zafi, domin yana tatse sauran maikon da yayi maki saura a jiki.
- Ki daina zama a cikin rana mai zafi.
- Kayan sawarki ya zama masu laushi ba masu gautsi ba.
- Ki daina yawaita barin jikinki a bude kar ma lokacin iska.
- Lebenki ya kasance ko yaushe cikin mai vaseline, ko lip gloss, banda yawaita sanya Jan baki.
- Idan zaki yi brush da safe har da lebenki ki ringa wankewa don hakan yana kara mai taushi sannan matacviyar fatar zata fita.
- Kinga shafa yoghurt ko madara a fuska, idan ta bushe sai ki wanke da ruwan sanyi
- Kada ki yawaita dirzar fuskarki, kuma ki daina yawan amfani da sabulu sosai.
- Ki yawaita amfani da man da akayi da dan itacen Apricot.
- Ki sayi Oats ki nika shi yayi laushi, idan zaki shiga wanka ki Debi cokali daya ki zuba cikin kofi daya na ruwan zafi, idan ya narke sai ki juye cikin ruwan wankan,
Sannan ruwan wankan ki ya zama ba mai sanyi ba ba kuma mai zafi ba.
- Idan kin gama wanka kada ki goge jikinki, ki bari fatarki ta shanye ruwan.
- Ki samu avocado wato piya, ki cire bawon ki dama yayi laushi, sai ki shafeta a fuska, kina lailaya fuskar taki a hankali, idan ya bushe sai ki wanke da ruwa mai sanyi sosai.
- Idan Zaki shiga wanka ki raba ruwan gida biyu, idan kika gama wankan sabulun sai ki shafa vaseline ko mankade sannan ki watsa sauran ruwan ajikinki. Idan kin fito sai ki kara shafa mai.
- Ki yawaita shafa ma fuskarki da hannuwa da kafafu mai bayan kowacce sallah don sunfi komai saurin bushewa a jiki.
- Idan zaki shafa mai a fuska ki lakuto kisa a dukkan hannuwanki ki shafa a fuska da hannu biyun har ko ina ya samu man.
Nan zamu tsaya, darasi nagaba zamu tsunduma cikin kwalliya da abinda ya kamata a shafa da wanda bai kamata ba saboda ingancin fata.
Comments
Post a Comment