Main menu

Pages

 


MASOYI ME FUSKA 2 YA FI MAQIYIN ZAHIRI ILLA..........


Duniya Makaranta.

Masoyi mai fuska biyu tabbas yafi makiyi illa a rayuwa. Masoyi mai fuska biyu baza ka taba game cewa ba masoyinka bane na gaskiya,. 


Sai ka zauna dashi da zuciya daya amma shi kullum damar ka yake nema. Sannan duk kyawun niyyarka sai ya san yadda yayi ya juyar da kyakkyawan niyya zuwa mummuna.


Sannan bazai taba yadda ya fahimceka ba komai gaskia abu da ya fito balo- balo- sai ya san yadda yayi ya cuss mummunar manufarshi a kanka.


Ga bayanin wata baiwar Allah da Tasha wahala itama aakan masoyan masu fuska biyu.


Babin da nafi Shan wuyar sa a Rayuwa shine Babin kasa Tantance MASOYI da MAQIYI,musamman Masoyi me Fuska 2,Haqiqanin Gaskiya Lamarin Masoyi me Fuska 2 akwai wahalarwa......


Masoyi me Fuska 2 zai maka iya soyayyar da ko wanda ya Haife ka zai iya gaza Nuna maka ita a zahiri,saboda yanda zai nuna maka Tsantsar Damuwa da Kulawa na Gasken Gaske,zai kasance me tsananin kirki Gareka,


Har zai mayar da komai nashi na ka ne,ko da Damuwarka itama ta shi ce,harma zai nuna maka Damuwar taka ta fi Damunsa fiye dakai,ba a Harshe zai faɗa ba,a zahiri ma hakan zai Aikata, 


sannan kuma zai Tabbatarwa da Duniya hakan,har sai Duniya ta yarda shi Halitta ne 1 Tamkar ya 1000,baza ka taɓa sanin waye shi ba,sai mu'amala me Tsawon Gaske ta haɗa ka dashi sannan za ka Fahimci waye SHI?


Da zarar ka Fahimci Gaskiya sai ya Barka da cizon Yatsa,da Nadamar Shiga cikin Rayuwarsa,da Nadamar shigo dashi cikin Rayuwar ka,sai ka Fahimci BARIKI ce,da Zamba cikin Aminci kuma munafinci madararta.


Ku sani ba dukkan Masoyi bane me fuska 2, Amma akwai su,cikin Mata da kuma cikin Maza,domin wacce na fara koyon wannan Darasin a wajenta shekaru masu Yawa baya MACE ce wacce shekarunta sun ninka Nawa,


ta yi Amfani da iya gejin Hankalina domin ganin ta cutar dani,duk da a zahiri kirkinta abin KOYI ne,Amma dole ta barni domin ba yanda ta iya dani saboda ba ita ta HALICCE Ni ba,


Amma maganin wannan matsalar shine GWARA A CUTAR DAKAI,DA ACE KAINE KA CUTAR,GWARA ACE Zuciyarka itace Farar domin ta Hakane cutar baza tayi Yawa Gareka ba balle ta maka Illar da zata hana ka sukuni.


Allah ya haɗa mu da Masoya na Gaskiya.Ameen.



SAƁAWA DA KUMA DACEWA A LISSAFI


Ni na ce: 5+5=10

Kai ka ce: 4+6=10

Shi ya ce: 7+3=10

Ita ta ce: 9+1=10


Dukkaninmu dai-dai muka faɗa, sai dai kowanne hanyarsa daban.


Don na saɓa maka baya nufin ni ko kai wani yana kan kuskure, aa saɓani ne na fahimta, wataƙila sakamakon duk ɗaya ne, girmamawa da mutuntawa tilas ne.


Mafi yawan matsalolinmu da abokan zamanmu suna afkuwa ne saboda abubuwa guda biyu:


1- Abin nufin da ba a fahimta ba.

2- Abin fahimtar da ba a nufa ba.


Hanyoyin magance waɗannan matsalolin guda biyu ne:


1- Ka nemi mutum ya fassara maka abin da yake nufi.


2- Ka kuma kyautata masa zato.


Allah maɗaukaki ya faɗi waɗannan hanyoyin a cikin Suratul-Hujurat:


*"فَتَبَيَّنُوا أَن تُصِيبُوا قَوْمًا بِجَهَالَةٍ فَتُصْبِحُوا عَلَىٰ مَا فَعَلْتُمْ نَادِمِينَ"*


الحجرات (6) Al-Hujuraat


_"Ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku afkawa waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma."_


*"يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِّنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ۖ "*


الحجرات (12) Al-Hujuraat


_"Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci mafi yãwan zato. Lalle sãshen zato zunubi ne."_


Taƙaitacciyar ma'anar da hakan ke nufi ita ce:


-Idan magana ta yaudare ni (Ta fito ba yadda nake nufi ba).


-Kai kuma kada ka bari fassararta ta yaudareka (Ka fassarata ba yadda nake nufi ba).


A yau mun yi sallah tare da wasu.

Gobe kuma wasun za mu yi wa sallah.


A duniya babu abin da ya cancanci mu tsaya muna saɓani a kansa, ko kuma mu riƙa gaba da juna a kansa.


Taken duniya shi ne: 


*(كُلُّ مَنْ عَلَيْهَا فَانٍ)*

_"Dukkan wanda ke kanta mai ƙãrẽwa ne."_


Taken lahira kuma shi ne:

*(خَالِدِينَ فِيهَا أَبَداً)*

_"Suna madawwama a cikinta har abada."_


Aikata alkhairi, ka yi afuwa, ka yi yafiya, ka kauda kai, ka nemi gafarar Allah maɗaukakin sarki, za ka rabauta.


Idan mukai la'akari da wanacan labarin na sama da wannan na kuskure fahimta to zamu iya nemo bakin zaren wajen al'amura mu na mu'amala da mutane.


Allah Ka dora mu aka dai dai, ka bamu ikon fahimtar dai dai, ka bamu ikon fahimtar yan uwanmu a dai dai, Kasa my zamto cikin mutane masu kyautata zato alan kowa. Ameen.

Comments