GIRKE-GIRKEN ZAMANI
Nikakken mangoro na musamman
Kayan aiki;
Mangoro
Condense
Madarar gari
Yoghurt
Ruwa
*Yadda ake hadawa*
Zaki samu mangoronki ki yanka ki cire bawon Saiki zuba a injin markade na hannu saiki zuba madarar gari, yoghurt, condense saiki markada ya markadu saiki zuba ruwa kadan ki kara markadawa, Saiki juye a kofi.wani dadin saima an gwad
GIRKE-GIRKEN ZAMANI
*Sweet potato croquettes*
Kayan aiki;
Dankalin hausa
Attarugu
Albasa
Mai
Citta/tafarnuwa
Maggi curry tumeric da sauran sinadaran dandano
Kwai uku
Cornflakes KO goldenmoon
*Yadda ake hadawa*
Farko zaki fere dankali ki yankata kanana sannan kiwanke ki zuba a tukunya sannan ki zuba ruwa kisa gishiri kidaura a wuta kidafa.
Bayan kin dafa sai ki tsane shi daga ruwan sannan kimursikata sosai da muciya ko whisker sai kidaura tukunya a wuta kisa mai kadan sannan kiyanka albasa kizuba aciki
kidan soya sama sama sannan ki jajjaga citta da tafarnuwa kizuba aciki sai kuma attarugu shima kizuba ki jujjuya sannan kizuba curry tumeric da sauran sinadarai ki jujjuya
Sai ki dauko kizuba akan dankalin bayan kin sauke ya huce sai ki jujjuya sosai komai ya hade a jiki sannan kirinka diban kadan kadan kina mulmulawa har ki gama
Sannan kisamo wani bowl kifasa kwan aciki kikada sosai sai kuma ki dan daddaka cornflakes dinki shima ki zuba a plate sai ki daura mai a wuta idan yayi zafi sannan
kidan rage wutan saboda kar ta kone wurin soyawa sai kirinka daukan kwallon dankalin kina somawa acikin ruwan kwai kina cirewa kisake sawa acinkin cornflakes din sai kisa amai kisoya. Shikenan aci dadi lfy.
GIRKE-GIRKEN ZAMANI
Potatoes finger
Wani nau'in sarrafa dankalin turawa
Kayan aiki;
Dankali
Kwai
Bread crumbs
Flour
Maggi
Gishiri
Yaji
Black paper
*Yadda ake hadawa*
Zaki dafa dankali da gishiri idan ya dahu sai ki sauke ki murmushe shi. Sai kisa maggi da black paper ki juya sai ki mulmula shi sai ki kada kwai da ruwa cokali daya sai kisa ma flour gishiri da yaji da black paper kadan
idan kin mulmula sai ki dakko kisa a flour sai kisa a kwai sai kisa a bread crumbs sai ki soya harse yayi golden brown shikenan se ci, za'a iya ci da ketchup ko sauce.
GIRKE-GIRKEN ZAMANI
Patera da miyan kwai
Kayan aiki;
Fulawa kofi uku
Sugar chokali babba daya
Gishiri rabin chokali
Mai chokali uku
Kwai biyi
Baking powder dan kadan
Ruwa
*Source*
Kwai hudu
Attaragu
Albasa
Mai
Tumatur guda hudu
Tafarnuwa da citta
Maggi da sauran sinadar girki
*Yadda ake hadawa*
Zaki tankade fulawa ki zuba a roba sai kizuba gishiri baking powder da suga kijujjuya sannan ki zuba kwai da mai ki mursikashi sosai komai ya hade sannan ki zuba ruwa ki kwabashi
Bayan kin kwaba sai ki rufe ki ajiyeta kamar minti biyar haka sannan ki dauko kisake kwabashi sai kirabata gida uku sannan ki murza dayan tayi fadi sosai
Sannan kisamo wani abu circle kicire shape din. Haka zakiyi tayi har kigama. Bayan kingama ki daura mai a wuta idan yayi zafi sai kirage wutan kadan sannan kisoya.
Source
Zaki daura tukunya a wuta sannan ki zuba mai kadan idan yayi zafi sai ki zuba albasa aciki kidan soyata sannan kijajjaga tafarnuwa da citta ki zuba akai kidan soyata
Sannan ki jajjaga attari ki yanka tumaturinki kanana ko kuma ki jajjaga idan kinaso sai ki zuba akai sannan ki zuba sinadaran dandano ki jujjuya kibarta ta soyu sosai
Bayan ya soyu sai ki kada kwanki ki zuba akai ki jujjuya kibarta na minti biyu sai ki sauke shikenan aci dadi lfy
Comments
Post a Comment