Main menu

Pages

 


DANBUM NAMAN KAZA

Duk iri daya ne da yadda kaeyin dambun naman rago da na shani.

Abubuwan Bukata

Albasa

Attarugu

Kaza 

Thyme

Maggi

Curry

Cumin

Cardamon

Bay leaf

Ruwa


Zaki dorasu akan wuta dukkansu ki barsu su dahu sosai da sosai


Bayan kazar taki ta dahu sai ki jujjuya sosai babu ruwanki da ruwan ciki karki ragesa domin zai kafe da kansa



Bayan kazar taki ta dahu sai ki jujjuya sosai babu ruwanki da ruwan ciki karki ragesa domin zai kafe da kansa



 Sai ki dakko muciya kokuma cokali na wood kiyita juyasu sosai da sosai zakiga naman yanata dagargajewa



 In kika cigaba da juyawa ruwan zai kafe amma kirage wutar kiyita juyawa


Kidai cigaba da juyawa sosai


Sai ki debo mai wadatacce ki juyeshi kiyita juyawashi baa barinsa har sai man kinga yafara kumfa to alamun yafarayi ne


Sai ki tsaneshi a abun tsanewa sai ki barshi yayi awa daya sai ki kwashe ki tsane nakasan da hannunki

 Amma nnso samu ne kiyi a non - stick frying pan saboda kar yayi maki kamu. Inkinaso sai kicire kashin aci lpya



SPECIAL IRISH

Ingredients

1.dankalin turawa

2.nama, kwai, tumatur

3.kabeji, bama , maggi

4.tafarnuwa ,man gyada


Da farko zaki fara fere dankalin ki ba tare da kin daddatsa shiba ki wanke saiki tafasa shi da ruwa da gishiri kadan, saiki kada kwai da albasa, curry, Maggi da tafarnuwa. 


Daganan saiki dinga tsoma dankalin kina soyawa, ki tafasa nama da maggi da gishiri d curry da tafarnuwa d albasa har yayi laushi sai ruwan ya kusa tsotsewa saiki kara wata albasa da timatur su nuna saiki kwashe. 



Ki yanyanka kabeji  kanana sannan a dafa kwai a yanyan kasa da dan girma sannan a zuba Maggi da bama a gaurayesa .



Sai a samu plate a zuba Irish a gefe sannan hadin namanki a gefe shima hadin kabejinki a gefe.



     DOUGHNUTS

Ingredients;

3 & half cup flour

1 tbspn yeast

1 tbspn powdered milk

1/2 cup sugar

2 tbspn butter

1 egg

Water as required



 -Zaki tankade flour a rubber me kyau kisa yeast, milk, sugar and egg ki juya


-Zaki rika zuba ruwa a hankali kina juyawa(kar yayi ruwa kar Kuma yacika tauri)har yahade sannan kiyi ta murza shi har na tsawon mintuna 5


-Sannan kisa butter kici gaba da murzawa har tsahon mintuna 30 yayi laushi


-zaki raba dough din ki murza shi kisa doughnut cutter ki fidda shape(in bakida zaki amfani da cup da murfin jarka)


-Ki barbada flour a tray ki rika jerasu har kigama


-Zaki rufe doughnuts dinki tsahon 40 minutes waje me dumi har su tashi


-kisa mai awuta har yayi zafi, kisoya har yayi  brown.



       YAM PAKORA


INGREDIENTS;

 Quater na karamar doya 

¼cup flour

½ tspn salt

½ tspn curry

½ spices 

1 nd half maggig

attarugu  

karamar albasa (1)

Oil 



-zaki feraye doyanki sannan kiwanke kisa a tukunya da dan gishiri har ta dahu


-Bayan ta dahu ki tace ki yanka doyan a tsaitsaye madaidaita, ki aje gefe


-Zaki juye flour ki a karamin abu kizuba mata seasoning and spices da grated attarugu da albasa sannan kizuba ruwa kina juyaws (kartai gudaji)da kauri(kwabin yafi na wainar flour kauri)


-Sannan kisa mai awuta in yayi zafi kidauko doyar da kika yayyanka kina sawa cikin kwabin flour ki jujjuya sannan cikin ma, .in ya soyu ki kwashe

 Ana iyaci da sauce, tea ko haka nan enjoy!



MIYAR CABEJI DA NAMA 

yadda ake miyar kabeji mai nama. Wannan irin miya tana kara lafiya a jiki sannan tana da dadi idan aka hada ta da farar shinkafa ko da dafaffiyar doya da kuma farar taliya da sauransu.



 Yana da kyau uwargida ta koyi yadda za ta rika canza dandanon miyarta a koda yaushe. Samun canji a dandanon girki na da alaka da irin kalar magi da kuma kayan kanshin da ake sa wa a lokacin girkin.


Abubuwan da za a bukata

Kabeji


Nama


Man gyada


Attarugu


Albasa


Tumatir


Magi


Kori


Tafarnuwa


Preparation:

Da farko za a samu kabeji sannan a yayyanka  manya-manya sannan a wanke da ruwan gishiri


 domin kashe kowace irin kwayar cuta da ke ciki sannan a yayyanka albasa da tumatir kwaya biyu kacal sannan a jajjaga attarugu da tafarnuwa.



Daga nan sai  wanke nama sannan a silala da albasa da gishiri kadan bayan ta yi laushi, sai a yayyanka kanana sannan a soya sama-sama. 



Bayan haka, a dora tukunya a wuta, a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da tumatir da kuma jajjagen attarugu da tafarnuwa a soya.



 Sannan a dauko naman a zuba ba tare da romon ba. A zuba magi da kori a gauraya a jira su tafasa sau daya sannan a zuba kabejin a gauraya a dan rufe. 



Bayan mintuna biyu, sai a sake budewa a gauraya sannan a rufe na tsawon mintuna uku sannan a sauke. 



ALKAKI MAI HAƊIN NAMA

INGREDIENTS

Nama niƙaƙƙa

Flour

Butter

Baking powder

Albasa

Curry

Maggie

Salt

Sugar


YANDA ZAKI HAƊA 

Dafarko uwar gida zaki tankaɗe flour wan ki haɗa da butter ki motse su wuri guda saiki sanya sugar da baking powder saiki kwaɓa irin kwaɓin meat pie,



 zaki ɗaura man gyaɗa akan wuta saiki sa albasa ki juye niƙaƙƙen namanki tare da albasa mai yawa kisanya Maggi da gishiri da curry kicigaba da juyawa har sai kinga ruwan dake fitowa ajikin naman ya tsane saiki juye ki ajeshi a gefe, 



saiki dauko flour ki murzata saiki ɗauko naman kina sanyawa acikin flour gefe gefen flour saikin linke saiki linkeshi kamar yadda akeyin alkaki saiki sanya acikin mai bayan yayi zafi saidai zaki rage wutar sai yayi jaaaa saiki tsame



SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.



Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.



Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.



Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya




Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.



Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments