Main menu

Pages





Asalin yadda ake operating computer tun daga farko, kunnawa da kashewa da amfanin kowane keyboard

 

 Kunnawa ko kashewa on/off

Idan zaka kunna computer zaka je can saman keyboard, anan power button yake, sai a danna slightly press not long press, saboda ita computer ba sai an danne da karfi take kawowa ba, kadan za a danna monitor dinta zai display.


Sannan idan za a kashe computer ba a power button ake kasheta ba, ta ciki ne ake kashewa, indai ba freeze tayi ba wanda ba wata hanya da za a bi wajen kashewar dole sai ta nan din.


Kashe computer directly daga power button yana haifar ma computer matsala, sannan duk wasu data da aka shigar ba zatayi saving dinsu ba, zasu goge. Don haka sai a kiyaye abi hanyar da tafi dacewa.


Don haka hanya mafi sauki shine; zaka je can kasa wajen start menu, kayi clicking anan kasa gefen hannun hagu kenan zaka ga shutdown sai kayi clicking shikenan.


Shi  'power button ana amfani dashi wajen kashe computer ne kawai lokacin da computer is freezes, ina kara kaddara maku, kuma ba wata hanya da za a iya kashewa sai ta nana din tunda cikin tayi hooking to shine kawai zaka danna "power button." To ammafa zaka iya rasa some data din dake ciki.


Keyboards: 

        Keyboard wato madannai na computer dake dauke da haruffa, number da sauaransu. Ana amfani da keyboard ne don yin typing, ma'ana rubutu a cikin computer. Kowane kalar rubutu zakayi to da keyboard zakayi shi.


Keyboard yana yanayin, ko ince kamanni da typewriter. Thohon abin rubutu kenan da akai amfani dashi a da caan kafin bayyanar computer. In appearance, yadda keyboard din computer take haka na typewriter take.


Bayan harafi da lambobi dake jikin keyboard akwai wasu muhimman keys da suka fi sauaran.


Amma kafin mu shiga wadannan ya kamata tun farko mu kawo maku kashe-kashen keyboard da muke dasu.

 1. Function keys (Muhimman keys)

2. Normal keys, ( keys din da aka saba dasu, saboda kowa ya sansu kuma yana amfani dasu a wayarshi)

3. Special keys (kebantattun madannai)

4. Direction keys ( madannai dake nuna sashes, dama, hagu sama ko kasa.)

5. Numeric keys( madannai masu dauke da lambobi kawai)

6. Numeric keypad( suma wadannan keys ne dake dauke da lambobi da kuma symbols)


Kafin mu wuce zuwa yin bayani daya bayan daya kan amfanin keyboard to zamu yi dan tsokaci akan ita kanta computer din.


Akwai Desktop computer sannan akwai Laptops computer.


Desktop computer itace wadda ake amfani da ita a ofisoshi da manya manyan kamfanoni da cafe cafe. Ita Desktop computer itace wadda ake dorawa bisa benci ko tebur wato (Desk) a turance.



Laptop computer itama ana amfani da ita a ofisoshi da kamfanoni har ma da cafe cafe din. But amfi amfani da ita a gidaje ko shago, ko ma'aikata dake karasa aiki a gidajensu.


Laptops computer itace wadda make dorawa bisa cinya wato ( Laps) a turance. 



Anan zamu tsaya sai a karatu na gaba zamu dora Insha Allah.



Comments