HUKUNCIN MAZAN DA BASA SON HAIHUWA SABODA TSORAN DAWAINIYAR 'YA'YA
TAMBAYA❓
MENENE HUKUNCIN NAMIJIN DA BAYASAN HAIHUWA SABODA TSORAN DAWAINIYAR 'YA'YA, MENENE HUKUNCIN ZAMA DASHI, SHIN MATARSA ZATA IYA BIJIREMAR TADAU CIKI BATAREDA YASANI BA?
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﻧﻌﻤﻨﺎ ﺑﻺﺳﻼﻡ .
AMSA👇
Shaik Usaimeen Rahimahullah yace:
Abunda yakamata ga Musulmi shine su yawaita nasabarsu gwar-gwadon yanda suka Samu iko, domin hakan shine Umarni da Annabi sallallahu Alaihi Wasallam ya fuskantar dashi zuwa Al'ummarsa cikin fadinsa ( Ku Auri mata wadanda kuke qauna masu haihuwa, domin nayi alfahari dayawanku ranar alkiyama,
Yawan dangi kuma shine yawan Al'ummah, yawan al'umma kuma shine izzarta da kwarjininta, kamar yanda Allah madaukakin Sarki yace: Yana gorantawa Banu Isra'ila
ﻭﺟﻌﻠﻨﺎﻛﻢ ﺃﻛﺜﺮ ﻧﻔﻴﺮﺓ، ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ، / ٦
Muka sanyaku Masu yawa cikin mutane
Annabi Shu'Aibu Alaihissalamu yacewa mutanensa.
( ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﺇﺫ ﻛﻨﺘﻢ ﻗﻠﻴﻼ ﻓﻜﺜﺮﻛﻢ ) ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ / ٨٦ .
Kutuna sanda baku dayawa Allah yayawaitaku.
Babu wanda yake inkarin yawan al'umma shine sababin izzarta da karfinta mai-makon yanda masu mugun zato suke suranta wadanda suke daukar cewa yawan al'umma shine dalilin dake kawowa Al'umma talauci da yunwa.
Lallai Al'Ummah intai yawa tadogara ga Allah, tai Imani da Alkawarinsa zai azurtata komai yawanta kamar yanda yazo cikin fadinsa
( ﻭﻣﺎ ﻣﻦ ﺩﺁﺑﺔ ﺇﻻ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺭﺯﻗﻬﺎ ..... ﻫﻮﺩ / ٦ .
Babu wata halitta face arzikinta yana wajan Allah
Face Allah ya saukake mata Al'amuranta ya wadatata daka falalarsa.
Dan haka bai kamata mace tai amfani da kwayoyin hana daukar ciki da sunan tsarin iyali ba saida sharudda guda biyu.
Nafarko: Yakasance tana cikin bukatar hakan dole, kamar bata da lafiya bazata iya daukar ciki kowacce shekara ba, komai siririn jikice ko kwan-kwaso, kotana da wasu ababe dazasu hanata daukar ciki kowacce shekara.
Na biyu: Mijinta yai mata izinin tasha, domin miji yanada hakkin akan 'ya'ya da daukar ciki, sannan dolene sai anshawarci likita akan wadannan kwayoyin, shin shansu yana cutarwa kobaya cutarwa.
Idan sharudda biyunnan suka cika, Babu laifi amfani dakwayoyin hana daukar ciki, Saidai hana daukar cikin nadan wani lokaci, bawai na din-din har abada ba, domin wannan akwai yanke yaduwar al'umma acikinsa.
fatawa Mar'atul musulimah ( 2/ 657-658).
Illah da cutar dashan wadannan kwayoyin suke haifarwa Shaik Usaimeen yace:
Labari ya iskeni daga bangarori dayawa daga likitoci damasu bada magani cewa kwayoyin hana daukar ciki suna cutarwa, tabangarenmu munsan illarsa, domin hana wani abu na dabi'ah da Allah yahalicci mutum akansa yakuma rubutawa matan 'yan adam babu kokwanto wannan cutarwane,
Allah madaukakin sarki mai hikimane, bahaka kawai yasa jini ke fita daka jijiyoyiba awani lokaci sananne saida hikima, kasancewar Mukuma muna hana haka da wannan magunguna cutane babu shakka.
Labari yariskeni abun yawuce yanda ake siffanta mana, yanasa lalacewar mahaifa, kuma yanasa cutukan gabobi, Wannan wajibine anisanceshi.
Tsarin iyalin da musulunci yayarda dashi shine wanda lalura tasa dole mace tadaina haihuwa, kodai saboda siranta kwan-kwasonta bata iya haihuwa dakanta, ko saboda wata cuta datasa dole tayi tsarin bisa sharudda biyun can da muka ambata.
Amma irin wanda yahudawa da 'yan bokoko suke tallatawa mutane wai ka qayyade iyalinka daka mace daya ko 'ya'ya uku zuwa biyar wannan haramunne yahudancine wajibine musulmai sutashi suyaqi wannan bala'in.
Babu inda yahalatta haka kawai saboda yahudanci ma'aurata su dena haihuwa wannan ba musulunci bane.
In suna so sudunga samun tazara daga haihuwa zuwa wata haihuwar Sai subi tsarin musulunci wajan Yaye yaro kada suke yaye yaro sai ya cika shekara biyu kamar yanda alqur'ani yabasu shawara.
Su dunga yin azalu ko mula masa inzasu biya bukatar sha'awarsu dan kada ciki yashiga wannan shine tsarin iyalin da musulmai zasu iya yi amatsayin tazarar haihuwa, ba irin wanda makiya Allah yahudawa suke fesa gubarsa cikin al'ummar musulmai ba, bisa da'awar hakan nakawo talauci da yunwa, Allah yai mana tsari daga makircin kafirai yahudawa.
mijin da bayasan haihuwa saboda tsoran dawainiyar 'ya'ya kibi duk hanyar data kamata kinuna masa addinin musulunci bai yarda da hakan ba, kuma ke yana cutar dake dan kinasan haihuwa, inkikai iya kokarinki yaqi kikabi duk hanyoyin daya kamata babu wani canji toki nemi yasakeki kawai babu Alkhairi atare da shi wannan mijin.
Bakiyi laifi ba idan kika nemi ya sakeki anan, kinemi kodai ya hakura kuci gaba da hayayyafa koya sakeki danke bazaki iya zama dashi ba.
Kuma ai ba shine zai azurtasu ba, Allah ne, kinuna masa shi su nawa ne agidansu ubansa shi kadai ko su biyu yahaifa amma ya akai yanzu kowa yana rayuwa iya wacce Allah yaqaddara masa na arzikinsa!!
Arzikinsu ba a hannunsa yakeba aikinsa yai tarbiyyarsu yadorasu akan hanya takwarai, shiriyarsu da arzikinsu yana hannun Allah wanda shine ya'azurta kafiri da zindiqi da jahilin dan bokon da turawa suka jirkita masa kwakwalwa.
Wallahu A'alamu.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .
SANARWA:
Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.
Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.
Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.
Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya
Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.
Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.
Allah Ya bamu sa'a.
Comments
Post a Comment