HUKUNCIN FAMILY PLANNING (TAZARAR HAIHUWA) A ADDININ MUSULUNCI.
Hakika malamai sunyi sabani akan halaccin yin family planning saidai an samu hadisai da suka nuna amincewar Annab (SAW) ga sahabbansa akan suyi azalu wato zubarda maniyyi yayin saduwa ba tareda ya shiga jikin macceba.
Ko shakka babu wannanma family planning ne, saidai inda malamai sukayi sabani shi yin family planning ta hanyar shan magani, duk da wannan sabanin wasu suna bada uzuri idan mahaifiyar na yawan daukar ciki
musamman wadanda suke daukar ciki sau biyu a shekara kuma wannan yakan haifar da rashin lafiyar yayanta. Rashin ingantacciyar lafiyar mahaifiyar, idan yakasance sai anyi operation a kowane haihuwa.
wannan wasu suna ga yana zama uzuri macen tayi family planning domin samun koshin Lafiyar ta da yayanta.
Amma wadanda suke yin family planning domin kauracewa haihuwa na har abada, tsoron talauci, kwaikwayon yahudawa, tsoron karyewar tattalin arziki, to anan malamai sunce baya halatta ayi family planning akan wadannan dalilan.
Yin Family planning ba shi daga cikin manufar aure a musulunci, hakika bayan haramcin yinsa haka kuma yana tattare da Matsalolin masu dinbin yawa.
Allah ya fada a cikin Alqur'ani Cewa, “Kada ku kashe ‘ya’yanku don tsoron talauci, Mu muke azurta ku ku da ‘ya’yan naku.”
Yahudawa maqiya addinin Allah ne suka kawo mana shi domin su rage yawan mu. Kuma duk wanda ya ke bincike ya san qasashen da suke zuga mu da mu yi Family Planing su ba sa yi.
Lalle yana daga cikin ni’imar Allah ga dan Adam da Ya ba shi ni’imar ‘ya’ya, duk wanda ya yi aure bai samu da ba, to baya cikin kwanciyar hankali.
Abin da zai qara nuna mana mahimmancin ‘ya‘ya shi ne yadda Manzon Allah (saw) ya yi wa Anas bin Malik (RA) addu’ar Allah ya ba shi yawan ‘ya‘ya,
Allah ya amsa addu’arsa ya ba shi ‘ya‘ya dari da ashirin da biyar (125). Lalle wannan kadai abin yiwa nazarine.
Idan muka koma gun Manufar aure ita ce domin a hayayyafa yadda manzon Allah (saw) zai yi alfahari da yawan mu ranar kiyama kamar yadda yazo a hadisi Cewa,
Wani mutumi ya zo wajen manzon Allah (saw)ya ce, “Ya RasulalLah na sami mata kyakkyawa ‘yar dangi amma ba ta haihuwa. Sai ya hana shi auren ta.
Ya qara dawowa karo na biyu ya qara maimaita maganar auren ta, amma Manzon Allah (saw) ya hana shi. Ya qara zuwa a karo na uku sai Manzon Allah (saw) ya ce masa, “KU AURI WADANDA KUKE SON SU SUKE SON KU (wadanda suka iya soyayya) MASU HAIHUWA DOMIN IN YI ALFAHARI DA YAWANKU A RANAR TASHIN ALQIYAMA”.
Musulunci addinine mai tausayi da jinkai hakika Malaman musulunci sunyi qiyasi (yarda) akan tsarin iyali, amma da sharadi;
Na Farko, Ya zamana Mahaifiyar bata samun isasshen lokacin da zata shayarda jaririnta.
Na Biyu, Ya Zamana Mahaifiyar na shan wahala wajen haihuwa, anan an yarda ta tsaya ta huta.
Hakika ajiye haihuwa don tsoron talauci Haramun ne, Domin Allah (swt) yana Cewa, "KADA KU KASHE 'YA'YANKU DON TSORON TALAUCI, MU MUKE AZURTA KU KU DA 'YA'YAN NAKU".
Wasu sukan ajiye Haihuwa wai don a samu isasshen lokacin tarbiyantar da yara, hakika shima wannan ya sabawa koyarwar Manzon Allah (saw).
Domin Sayyidina Anas bin Malik (RA) ya shekara dari da hamsin (150) a duniya, saboda dadewa har sai da ya makance.
Yana cikin makantar tasa ne ya kira babbar ‘yarsa mai suna Umainatu ya tambaye ta yawan ‘ya’yansa. Sai ta ce sai an qirga. Da aka qirga ne aka samu dari da ashirin da biyar kuma duk sun hardace Qur’ani.
Shin idan yawan 'ya'ya na saka a kasa tarbiyan tarda 'ya'ya ya Sayyidina Anas ya yi da 'ya 'ya har guda dari da ashirin da biyar (125) kuma duk mahardata qur'ani? Babu shakka wannan kalubalene ga iyayen mu masu wannan rubabbar dabara.
Wallahu A'alam
SANARWA:
Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.
Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.
Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.
Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya
Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.
Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.
Allah Ya bamu sa'a.
Comments
Post a Comment