Main menu

Pages

HUKUNCIN ZOBEN FAMILY PLANNING

 

HUKUNCIN ZOBEN DA MATA KE SAWA NA FAMILY PLANNING.


Akwai wani zobe da ya fito wanda ale siyarwa mata a matsayin idan suka sanya shi to baza su samu ciki ba.




Wato wannan zamani da muka shigo wallahi mata muyi hattara musan irin abinda ya kamata muyi.




Idan ba haka ba kuwa  to zamu kai kanmu ga halaka. Saboda wataran sai mun fada komar aikata tsafi ko amfani da kayan da aka tsafa ko akai mashi surkulle.




Kunga kenan girls ta shigo, kuma idan aka mutu a haka wuta ce tunda Allah ba Ya yafe shirka.





An yi tambaya game da wannan zobe na family planning a tashar Africa TV3 a filin su na Fatawa.





Sheikh Abdulwahab Abdallah shine ya amsa fatawar, inda akace ko ya halatta sanya wani zobe da ake siyarwa na family planning?




Malam yayi mamaki yace wane irin zobe kuma, ni ma lokacin ban taba jin cewa akwai wannan zobe ba sai cikin kwanakin nan da naga ana tallansa.




To Malam yace wannan shirka ne, saboda dole ne cikin zoben a samu surkulle a ciki.




Zobe haka kawai a Sanya a hannu kuma ya hana daukar ciki, naji ma wasu na cewa sharadinsa kar a bari ya fadi kasa.




Kenan tun a nan ya kamata mu gane cewa akwai kaucewa a ciki. To a takaice dai Malamai sun nuna cewa sanya wannan zobe haramcin ne kada'an.





Don haka sai mu kiyaye. Sannan ina kara Jan hankali ga masu saye da masu siyarwa da muji TSORON Allah mu kauce ire - iren wadan nan abubuwan.




Sannan banyi wannan rubutu da wata manufa ba, ko don kashe ma masu sana'ar kasuwa, a'a nayi haka ne kawai don in jawo hankalin 'yan uwa musulmai don mugudu tare mu kuma tsira tare.





Rayuwar Duniyar duka nawane dole wataran zamu wuce zuwa inda bazamu taba dawowa ba.





Akwai abubuwa ire - iren wannan zobe da keyin ayyuka mabambanta. To koma dai na menene mu kiyaye mazanmu da matanmu.



Allah Yasa mun dace da dukkan alkhairi.



SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.



Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.



Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.



Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya




Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.



Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments