Jiya Ba Yau Ba. Allah Sarki Fati Muhammad kenan a firan da akai da ita a BBC.
Zan yi amfani da wannan damar inyi Jan hankali ga mata 'yan uwana. Walau 'yan fim ko ba 'yan fim ba.
Ita mace rayuwar ta gajerace, ba kamar namiji ba, don haka duk abinda zakiyi ko ki zama to wallahi na dan lokaci ne.
Zanyi kwatanci da Fati Muhammad ba don tozarci ko don cin fuska ba, a 'a kawai zanyi misali da itane don duba da tashe, da daukakar da ta samu a lokacin ta, wanda tarihi ya nuna tun daga jiya har zuwa yau babu wata yarinyar film da tayi tashen ta.
Amma gashi yau da ranta da lafiyarta tana ji tana gani yau da gobe sun shiga tsakaninta da wannan shura da daukakar da tayi saboda girma da ya kamata har ya bayyana a kan fuskarta.
Allah Sarki jiya ba Yau ba. A kalla Fati Muhammad kinci ribar rayuwar tashen da kikayi, saboda a lokacin ki tashen da daukakar kin same ta ne ta tsarkakkiyar hanya.
A wancan lokacin Matan kannywood suna suturta kansu Suna kokarin kare mutuncinsu, shiyasa a wannan zamani da wasu 'yanmatan ke neman daukaka ta hanyar bayyana tsiraicinsu, da nuna zallar rashin kunya shaharan tasu bata zuwa ko ina.
Duk wani wayewa da zaku na takama da ita, baki kai Fati Muhammad ta wancan zamanin ba, duk wata daukaka da zaki takama da ita ko cikon cokalii ba ki kai ba idan an danganta ta da irin ta Fati Muhammad.
Ashe ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali yayi wanka ya fita tass. Ita da tayi na ta tashen cikin tsabta da taka tsantsan, wadda kuma da itane aka gina kannywood har ta zama abinda ta zama a yau, gashi ta koma gefe tana kallo duk da wannan gudummuwa da ta bayar.
Wadda da ita ne aka assasa kannywood har yau ku 'yan baya kuka zo kuna shirme da rawan kai wanda ba wata gudummuwa da kuka bayar sai ma kokarin rusheta da kuke yi har zaku zo kuna feleke.
To wallahi ku taka a sannu, kubi a hankali kuji tsoron Allah Ku kiyaye hakkokinsa Ku kare mutuncinku a matsayin Ku na diya mata.
Yanzu ga Fati Muhammad bata da buri a rayuwarta irin ta samu mijin aure na gari ta zauna cikin dakinta kamar kowacce mace.
Yanzu wannan bai zame maku ishara ba, ita fa nata yayi kyau kenan, duba da yadda tayi nata tashen a tsabtace a mutumce ba tare da fitar da tsiraici ko rashin kunya irin taku ba.
Da ita aka gina kannywood din da kuke takama, kamar yadda Ali Nuhu yake sarkin kannywood wallahi in har adalci za ayi to Fati Muhammad itama ya kamata a bata sarauniyar kannywood, ko da ba ta cikin masana'antar ya kamata ayi mata alkunya da wannan sarauta.
Fatima Muhammad mina taya ki addu'a Allah Ya baki Miji nagari na kwarai, tare da zuri'a ta gari ta kwarai alfarmar Annabi Muhammad SAW. Allah duk wasu kimtsattsun Mata salihai da basu da miji suke neman nagari, Allah Ka dubesu diban Rahama Ka karba masu
To wannan dai Jan hankali ne gare Ku 'yan Matan kannywood da sauran Mata Ku ribaci rayuwarku tun kafin lokaci ya kure.
Comments
Post a Comment