Matakan Da Ya Kamata A bi Wajen Daukar 'yar Aiki, Ga Masu Daukar 'Yan Aiki
Mata da yawa suna tafka wasu kuskure da ya kamata a ce sun gyara. Ko wacce mace ta kan so ta rinqa samun hutu a cikin gidan ta.
musamman idan mijin ta ko ita kanta tana da halin ďauko mai aiki. Amma yanzu abubuwa sun juya don masu aiki sun jefa wasu mata cikin tasku da tashin hankali.
Haka nan samun wadannan labarai ya sanya wasu jin tsoron ďauko mai aiki ko da kuwa aikin gidan su zai kashe su.
In kina da buqatar ďaukan mai aiki sai ki biyo ni don sanin abubuwa da dama akan ‘yar aiki.
Wannan rubutun da yardan Allah zayyi bayani dallah-dallah kuma mata zasu fahimci abubuwa dayawa da suke yin sake dasu.
Farko dai WACECE MAI AIKI? Mai aiki dai zamu iya cewa baiwa ko bawan wannan zamani ne, banbancin shine wannan kamar hayansa kake yi
wancan kuma siyan shi kake yi mallakin ka ne. Mai aiki ‘yar adam ce kamar ki, hanyar da aka bi aka same ki ita ma shi iyayen ta suka bi suka same ta.
Tana da uwa da uba da ‘yan’uwa kuma suna son ta kamar yanda naki iyayen suke sonki.
Mace ce ita kamar ki, kuma zata iya yin duk abun da kike yi a cikin gidan auren ki koda kina ganin bata waye ba.
Saboda mutum ba dabba bane yana da hankali da tunani.
Masu aiki sun kasu kashi biyu, mai zuwa kullum da kuma wadda take zaune a gidanki.
1. Mai aikin zuwa kullum: Wanda kun qayyade lokacin da zata zo aiki da lokacin tashin ta.
Wata ma ba kullum bane kin bata ranakun zuwan ta. Irin wannan sai in tana unguwar ku a kusa da gidanki.
2. Mai aikin kwana: Itace wacce ake ďaukota zama dindindin, a kwana a tashi da ita, ta zama part of your family.
Irin wadannan musamman daga wani gari ake ďauko su a kawo su aiki.
Binciken mai aiki kafin a dauko ta.
Shin kin taba tunanin kafin ki ďauko ‘yar aiki ki yi bincike a kanta? Da ita kanta mai ďauko masu aiki.
To bari ki ji, in zaki ďauki mai aiki akwai abubuwan da ya kamata ki duba kafin ta shigo miki gida, ga su kamar haka:
1. Asalin mai aiki: A binciki asalinta, shin iyayen ta mutanen kirki ne. Sannan a binciki in da aure ko ba aure aka haifeta.
A binciki tarbiyyan gidan su da irin abun da mutanen unguwa suke fadi game dasu.
Domin rashin duba asalin ďan aiki ya ‘bata aure da dama domin baki sani ba ko gidan mayu ne ko matsafa ba a ďauko masifa a kawo miki gida.
2.Tarbiyyan yarinyar a unguwar: Ba ko wane ďan qauye bane bagidaje kuma qauyukan da da yanzu akwai banbanci.
Zaki ga yara qanana amma suna zina, sai a kawo ta kina ďauka bata san komai ba, bayan ta girmeki a harkan don ita ba da namiji ďaya take yi ba.
Tana zuwa gidan kuma bata fita, gashi tana ci tana qoshi sai ta fara neman mijinki ko ‘ya’yanki. Don haka In ‘yar iskace ki canza wuri.
3.Addinin yarinyar: Ki tabbata an kawo miki wacce take zuwa islamiyya ko ba boko don ki samu sauqin wasu abubuwan.
Idan jahila ce zaki sha wahalar zama da ita. Kuma zata iya cutar dake don ba tsoron Allah a ranta.
4.Ki san full address ďinta: Ko kuma ma ki je qauyen su in kina da lokaci kije har gidansu, KUMA kisan wasu daga cikin danginta.
An sha samun masu aikin da suke tafka sata, wata har yara ta sata ta gudu dasu, saboda babu wanda yasan daga ina ta fito.
Amma in ta san an san gidan su da qauyen su zata rinqa tsoron yin wasu abubuwan.
5.Lafiyar yarinyar: Kada a kawo miki mai aljanu su zo su shafi ‘ya’yanki, ko mai wata cuta da zaku iya kamuwa dashi.
Idan wacce take unguwar ku ne yin binciken ta zai fi miki sauqi. Wannan da ma wasu yana da kyau ace an kiyaye su.
Kuskure ne ki ďauko wanda baki san komai game dashi ba ki a aje a gidanki.
Kada ku manta ana gadon mummunan hali da ďabi’a, kamar yanda ake gadon halin kirki da mutunci.
Idan kika yi sake zaki sha mamakin mai ‘yar aiki zata aikata miki wata rana. Na ga wani video a instagram da matar ta cewa yarinyar ta tafi ta gaji da ita, har zata fita sai ta ji hankalin ta bai kwanta ba da aka bude jakan kayan ta sai ta ga hotunan ta dana ‘ya’yanta.
Kuma da aka bincika tafiya zata yi a musu asiri, kin ga wannan ba abun wasa bane. Ta tafi amma ta sa ana turo miki da fitintinu a gidanki.
Anan zamu tsaya akan wannan maudu'i. Mu tara gaba a kashi na biyu na wannan darasi. Mata mu kiyaye.
SANARWA:
Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.
Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.
Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.
Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya
Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.
Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.
Allah Ya bamu sa'a.
Comments
Post a Comment