Main menu

Pages




 DAMBUN NAMA

Ingredients

Nama

tarugu

albasa

tafarnuwa

citta

masoro

maggi

nutmeg

mai

 Yadda ake hadawa

Zaki samu tsokar nama me kyau ki yanka shi kanana ki wanke sai ki sa a tukunya ki yanka albasa sosai ki sa maggi da gishiri sai ki daka ginger sa garlic da black pepper da nutmeg ki zuba su ki sa ruwa ya sha kan naman ki rufe ki do rashi ya dahu sosai



 ki sa wuta kadan saboda in wuta yayi yawa a abu baya dahuwa sai kin tabbatar namanki ya yi luguf kina tabawa yana rugujewa ki juye a turmi ki dakeshi yayi luguf sai ki juye a tray yasha iska.



ki daka tarugu da albasa da garlic suyi laushi ki hada da naman ki ki cakuda ki zuba  spices kadan sai ki sa oil a pan yayi zafi ki zuba kita juyawa har sai ya soyu (ba suyar cikin mai ba ne)sai ki juye shi a kwando zai tsane kuma yasha iska sai ki juye a tray ki bazashi yana shan iska shikenan.

Akwai dadi kuma ko yaushe zai kai bazai lalaceba



𝗖𝗛𝗜𝗡𝗘𝗦𝗘 𝗖𝗛𝗜𝗖𝗞𝗘𝗡 𝗙𝗥𝗜𝗘𝗗 𝗥𝗜𝗖𝗘


Kayan da ake bukata

Shinkafa {3cups}

Man~gyada {6tbsp}

Carrot {2}

Peas {1/6cup}

Tattasai {2}

Green pepper {2}

Chicken {1}

Egg {2}

Soy sauce {1/6cup}

Mangyada

Yadda ake hadawa

   Da farko ki tafasa shinkafa ki cire starch din saiki yayyanka duk abubuwan dana lissafa diced shape,cube,carrot, chicken,tattasai, ki ajesu agefe saikisa mangyada da albasa awuta inya soyu kisa soy sauce 2tspn da kazarki da kika tafasa ta kika yayyanka ta cube ki soya na zuwa 5mnts 



ki zuba tattasai, peas da duk sauran abubuwan da kika yanka ki qara soyasu na 5mnts saiki zuba shinkafar kita jujjuyawa saiki zuba ruwan tafashen kazar kadan ki rufe hartayi



sai kiyi scrambled egg ki zuba akan shinkafar ki zuba sauran soy sauce dinda dan maggi kadan yadda zai dauka ki rufe ya ida 



      AWARAR WAKEN SUYA

Abubuwan  hadawa

Waken soya

attarugu

albasa

ruwan tsami ko dan tsami

dandano

 Yadda ake hadawa

Da farko zaki jika wakenki idan ya jiku, sai ki kai a markado miki.


Idan an kawo daga markade sai ki dan diga manja aciki, ki dan kara ruwa saiki tace.

Idan kin gama ki zuba a tukunya ki dora a wuta.

Sai ki dauko attarugunki ki jajjaga ki yanka albasa.



Ki dinga kula da wannan ruwan awarar da ki ka dora idan ya fara tafasa saiki dauko ruwan tsaminki ki zuba a ciki, za kiga duk ta hade jikinta



Sai ki zuba albasa da attarugu da dandano aciki, idan ta dan kuma dahuwa saiki samu abin tata ki juye awaran a ciki ki daure shi sosai ki samu abu mai nauyi ki danne ta ko kuwa ki rataye yadda ruwan zai dige daga jikin awaran.



Idan kin tabbatar ruwan ya gama digewa sai ki yayyanka ta dai dai girman da kikeso sai ki dora mai a wuta ki fara suya.



       DAMBUN COUSCOUS


ingredients::


couscous 2cups

1/2 Dakakkiyar gyada

1 Mangyada

ganyen zogale 

attarugu

albasa 

seasoning cube

spices( black pepper onga, mix spices, curry)

salt

Ruwa daidai misali

Yadda ake hadawa

zaki samu babban bowl kizuba 2cups na couscous dinki seki zuba groundnut ki juya kikawo Oil dinki ki zuba attarugu da albasa ki wanke zogalenki kizuba ki juyasu su hade jikinsu 



sai ki zuba seasoning cube ki zuba spices ki juya ki saka gishiri kadan ki dandana idan komai yayi shikenan seki yayyafa ruwa one cup akai kisake juyawa ...

    


   kidora ruwa a steamer ya tafasa seki dauko buhunki me tsafta ki juye hadin dambunki aciki ki nade kisaka acikin steamer dinki kirufe ki tabbatar turirin bayafita sekiyi steaming zuwa 35-40minutes kibude kitaba zakiji yayi laushi seki sauke..



SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.



Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.



Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.



Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya




Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.



Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments