Main menu

Pages

RUWAN ZAFI DA NA SANYI WANNE YAFI GA MACE?

 

TSARKI DA RUWAN SANYI KO NA ZAFI WANNE YAFI AMFANI, KUMA WANNE KE DA  ILLA GA LAFIYAR MACE



Za muyi bayani akan amfanin ruwan sanyi da na zafi, ga lafiyar Mace.




Mafi yawancin binciken da kikitoci sukayi shine tsarki da ruwan dumi yana da matukar amfani wajen tsabtace gaban Mace.





Dalili kuwa shine, a ka'ida  ana so Mace ta yawaita wanke gabanta a kalla sau daya zuwa biyu a rana.




Sannan kuma ba a son mace na tsarki da kowane irin sabulu  saboda akwai subulai masu karfi sosai.




Yin tsarki da sabulu mai karfi yana kashe virginal bacteria wadda ke da amfani kuma da kariya a cikin Virgina.



Har ila yau, yin hakan yana jawo kaikayi ko burning sensation idan karfin chemical ko fragrance dinsu ya bata ph balance din Virgina.




To idan har haka ta faru kuwa to akwai yuwuwar infection ya shiga kamar irin yeast infection ko bacterial virginosis.




Duba da haka ya sanya masana bincike sukace Mata su daina amfani da duk wani sabulu in ba ordinary soap ba.




Amma abinda yafi inganci shine suyi amfani da zallar ruwa wajen tsabtace gaban su don kare kai daga cuta.




To duba da wannan ne masana suka karfafa yin tsarki da ruwan dumi, don sai yafi fita sosai fiye da yin amfani da ruwan sanyi ko da babu sabulu.




Shin Amfani da Ruwan Zafi ya na Tsuke Mace?


Amsar ita ce a a, babu wani bincike da ya tabbatar da hakan a likitance, sai dai ya tabbata cewa yana da matukar amfani wajen safe cleaning.



To shi Kuma ruwan Sanyi meye illarsa?


Naturally ruwan sanyi bashi da wata illa don Mace na amfani dashi wajen yin tsarki.



To ammafa idan overall din tsabtar mace ta gaza to zai iya yuwuwa ba zata taba rabuwa da ƙanana matsaloli ba, na virginal irritation ko minor infection.



Ya maganar da akecewa ruwan sanyi na bude gaban Mace wasu suce yana Tsuke shi.




Wannan ya danganta da yanayin fahimta,  amma abinda yake a zahirance shine dukkan su,  (ruwan zafi da na Sanyi) naturally babu mai bude Mace ko tsuke ta.



Amma ana iyayin kiyasi saboda dabi'unsu lokaci zuwa lokaci.



Ruwan sanyi yana takura cells din jikin mutum, don haka akwai yuwuwar ya iya taimakawa wajen tsuke gaban Mace ya dawo tsaka tsaki (average) idan an mayar da hakan dabi'a.




Ruwan dumi kuma yana wartsake cells din mutum ne, sannan yana iya sanitizing.



Don haka idan aka amfani dashi dabi'a to zai iya kore zaman datti ko kazanta mai iya kawo infection.



Duk wannan bayanin da ake tayi kan tsarki tsarki, ana nufin wanke ta wajen (vulva area) ba a wanke can ciki (Virginia).



Naturally Allah Ya yi wannan waje  mai zaman kansa wajen tsabtace kansa da kansa, tare da ordinary normal discharges.





Rashin sanin yadda ya kamata a tsabtace  gaban yasa mata da yawa basu rabuwa da virginal infection.



Ba don komai ba sai don rashin sanin yadda ya kamata a wanke wajen yadda ya dace ko iya tsarki yadda ya kamata.



Idan kinzo zakiyi tsarki ki fara wanke gaba kafin baya, sannan idan kina tsarki idan kika dora hannunki to kita zuba ruwa kina wankewa ba tare da kin daga hannun ba.



Yin hakan kamar kinayin flushing ne, amma idan kinayi kina dagawa to kina kara dankara najasar ne a jikinki saboda akwai sauran ta a hannunki, kuma kar kina tsarki ki ringa hada gaba da baya kina wankewa, yin hakan kina janyo wa gabanki kwayoyin cuta.

 



Don haka Mata sai ku kiyaye a ringa kula sosai. 


.

SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.



Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.



Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.



Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya




Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.



Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments