Main menu

Pages

A matsayin ki na Mace ko kinsan wannan Amfanin na Ruwan Dumi



Amfanin Ruwan Dumi Ga Ya Mace.

Mafi yawan mata ba su damu da yin amfani da ruwan dumi ba, to lallai daga yau ki sani cewa ruwan dimi na da matukar mahimmanci ga jikinki.



 Ruwan dumi yana kara wa mace lafiya a jikinta fiye da jikin da namiji. Idan da baki yin amfani da ruwan dumi a jikinki, to daga yau ki fara za ki sha mamakin yadda jikinki zai koma.



1. Ruwan dumi: yana taimaka wa mace wajen kashe mata wasu kwayoyin cuta idan tana tsarki da shi. Yana kuma kara mata ni’ima a matsayinta na matar aure.



2. Ruwan dumi: yana zama kariya ga mace wurin kamuwa da cututtuka idan tana yin wanka da shi. yana kuma gyara wa mace fata ta yi kyalli ba tare da kin yi bilicin ba.



3. Ruwan dumi: yana mikar da hanjin ciki lokacin da suka tattari sakamakon yunwa ko kuma an yi azumi. Ina bukatar idan mutum ya dade bai ci abinci ba, to idan ya zo zai ci ya fara da abu mai zafi domin ya mikar da hanjinsa kafin wani abincin da bai da zafi.



4. Ruwan dumi: yana kara dankon zamantakewar aure, idan mace tana yin tsarki da ruwan dumi yana kara mata ni’ima ta yadda mijinta zai gamsu da ita.



5. Idan mutum; yana shan ruwan dumi yana kara wa na’urar jiki lafiya. Yana kara wa jikin karfi da walwala ta yadda kowani bangare yayi aiki yadda ya kamata.



6. Shan ruwan dumi: yana kara karfin makwogoro, ta yadda muryar mutum zai fita kamar wajen karatu ko kuma wajen bayani ta yanda mutane za su fahimta 



Don haka Mata a dage wajen amfani da ruwan dumi a koda yaushe don samun cikakkiyar lafiya, da kariya daga wasu cututtukan.



SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.



Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.



Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka kabi dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.



Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya




Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.



Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments