AMFANIN SABARA GA JIKIN DAN ADAM.
Ganyen sabara yana taka muhimmiyar rawa sosai a rayuwar dan Adam, wanda mutane da yawa basu sani ba. Ga kadan daga ciki.
Matan kasar Hausa na yin amfani da ganyen sabara idan suka haihu, Inda suke daka ganyen suyi kunun gero suna sha domin karin ruwan nono da inganta lafiyar ciki.
Ana amfani da garin ganyen sabara don warkar da ciwon daji (Cancer).
Ganyen sabara na maganin kumburin jiki da kaikayi.
Ganyen sabara na maganin kurajen fuska da na kazuwa masu kaikayi da zafin jiki da na ciki.
Ganyen sabara na maganin tarin asma da na tibi (tuberculosis)
Ana gauraya garin sabara da garin bawon bagaruwa don maganin kuna a jiki.
Ana hada ganyen sabara da wasu ganyayyakin itatuwa a tafasa ko a daka a mayar dasu gari don maganin Basir, gudawa, cututtukan ciki, farfadiya, ciwon gabban jiki, hawan jini, da sauran su.
Ana amfani da danyen ganyen sabara da na nunu a tafasa, mace mai jego ta rinka surace dashi hakan zai Kara mata lafiya da karfin jiki.
Ana tafasa saiwar sabara a tace a sha ruwan don maganin tsutsar ciki
Ana tafasa saiwar sabara da kirya a zauna a cikin ruwan don maganin Basir mai sa kaikayi, ko kuraje ko Basir mai tsiro
Ana tafasa ganyen sabara a ringa kuskure baki dashi don maganin kurajen cikin baki.
Asha cokali daya na garin sabara a cikin nono, don maganin Dankanoma.
Mai fama da kurajen makogwaro ko ciwon makogwaron, sai ya tauna danyen ganyen sabara ya hadiye ruwan.
Allah Ya karemu da lafiya mai amfani mai dorewa ameen. Allah Ya sa a dace.
SANARWA:
Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.
Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.
Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.
Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya
Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.
Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.
Allah Ya bamu sa'a.
Comments
Post a Comment