Matakin Daura Damarar Hana shigowa da Allurar Rigakafin Covid-19 Ta Jabu a Nijeriya.
Gwamnati Nijeriya tayi wa jama'a matashiya akan Labarin da ake yadawa na shigo da Allurar rigakafin covid-19 ta Jabu da akace za a shigo dasu Africa.
Hukumomi sun kawar da fargaba da taraddadin cewa ana bada rigakafin cutar covid-19 na Jabu wanda yake cutarwa ko wasu hukumomi da ba a basic izni ba suna siyar da rigakafin.
Darektan hukumar kulanda ayyukan asibitoci Adebimpe Adebiyi, a ma'aikatar Kiwon lafiya ta tarayya, ya fitar da wata sanarwa akan wannan batu.
Sanarwan ta biyo bayan wata wasikar da kwamitin shugaban kasa mai yaki da Covid-19 ya fitar game da gano batun dubban allurar rigakafin ya Jabu da za a shigo da ita Africa daga China.
Adebiyi yace, kafin a iya hana shigowa da rigakafin ta Jabun ya kamata ma'aikatar kwastam ta Nijeriya da ta kebe filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Nmandi Azikiwe a Abuja a matsayin hanya daya tilo da za a rika shigar da Allurar rigakafin a Nijeriya.
Gwamnati taja hankalin darektocin Kiwon lafiya a asibitocin tarayya da sauran hukumomin Kiwon lafiya akan wannan batu.
Nijeriya ta samu zubin rigakafin miliyan 3.94 na rigakafi na kasa da kasa na COVAX a farkon watan Maris.
Comments
Post a Comment