YADDA ZA KI LURA DA KANKI LOKACIN AL'ADA
Sau da dama a lokacin jinin al’ada mata kan shiga halin tasku, inda wadansun su kan kaurace wa shiga cikin mutane, wanda kuma ke takura wa rayuwarsu har su samu kansu kamar an sanya musu takunkumi.
Hakan ne ya sanya a wannan makon zan yi miki bayanin yadda za ki lura da kanki a lokacin jinin al’ada har ki samu sakewa da kuma walwalawa.
Kwantar da hankali
Ba a so ki tayar da hankalinki don kin fara ganin jinin al’adarki, hakan zai sanya a fahimci halin da kike ciki. Don haka ki kwantar da hankalinki kamar babu wani abu da yake faruwa da ke.
Ki kasance dauke da ‘Pad’ ko ‘Tampon
a kowane lokaci don guje wa jin kunya.
Canza ‘Pad’ da ‘Tampon’
Ya kamata ki rika canza ‘pad’ ko ‘tampon’ duk bayan awa 4 zuwa 8, idan kuma jinin yana zuba sosai sai ki rika canzawa lokaci zuwa lokaci, kuma lokacin da jinin ya gama jika ‘pad’ ko ‘tampon’ din. Barin ‘pad’ ko ‘tampon’ ya dade zai sanya samuwar kwayoyin cutar bacteriya, wanda hakan kuma zai haifar miki da matsala.
Lura da kai
Daga lokacin da aka ce an fara al’ada, tsabtace kai na da matukar wahalar gaske. Musamman lokacin zafi, daga an yi gumi sai a fara wari mai tayar da zuciya, har mutane su rika kyamar wacce ke jinin al’ada.
Don gujewa hakan sai ki rika wanka lokaci zuwa lokaci, hade da shafa turare mai tafiyar da wari (deodorant), sannan ya kamata ki goge bakinki sau biyu ko uku a rana domin hakan zai magance miki warin bakin da ke fitowa daga baki lokacin jinin al’ada. Bayan haka ki rika cin cingam mai kamshi, ko tsotsar minti ko cin cakulat.
Lura da kurajen fuska
Wadansu matan idan za su fara ko kuma sun fara jinin al’ada kurajen kan fito musu, to idan kina daya daga cikin wadannan matan, idan kurajen sun fito miki, kada ki fasa su, ko kuma ki rika taba su. Abin da za ki yi shi ne, ki rika wanke fuskarki sau biyu ko uku a rana. Ko kuma ki wanke fuskarki daga zarar kin fara gumi idan lokacin zafi ne.
Lokacin al’ada
Yawancin kwanakin al’ada ba sa wuce 3 zuwa 7. Duk lokacin da jinin al’ada ya zo miki to za ki samu na gaba ya zo a wani lokaci daban, duk da cewa wadansu kan samu tazarar kwana 28 ko 35 kafin wani jinin ya zo musu.
Don haka ina ba ki shawara ki ajiye karamar kalanda a dakinki ko ki saita kalandar cikin wayarki. Hakan zai ba ki damar fahimtar lokutan al’adarki, kuma zai ba ki damar lura da kanki ba tare da wani ya gane ba.
Jin zafi
Lokutan al’ada kan zo da ciwon ciki, ciwon kai ko murdawar mara, hakan kan sanya takura, hanyar da za ki rage hakan shi ne ki rika motsa jikinki, misali ki rika kai ziyara ga ‘yan uwa da abokan arziki, amma idan ciwon cikin ko kai ko kuma murdawar marar ta tsananta sai ki nemi likita.
Allah Yasa min fahimta, ya kara mana lafiya da saukake mana matsalolin Al'ada. Ameen
SANARWA:
Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.
Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.
Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.
Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya
Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.
Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.
Allah Ya bamu sa'a.
Comments
Post a Comment