AMFANIN LALLE DA MAGUNGUNAN DA YAKE YI.
Lalle wanda muka sani a kasarmu ta Hausa wata bishiya ce da mata suka fi yawan amfani da ganyenta musamman dan yin kwalliya a lokutan bukukuwan aure.
A nan ba ina nufin lallen da ake yin zanen jiki na siffa ba, ina nufin lallen da muka sani na gargajiya da aka daina yin sa musamman a wannan lokacin.
Ita dai bishiyar lalle tana da ganye launin kore da hure da kuma sayyu, wadanda dukkanin su ana amfani da su a sarrafa a yi magani da shi. Ganin yanda wasu sun dauki lalle tamkar kayan ado na mata kawai wadanda ko su a yanzu sun daina yin lallen nan na gargajiya da na ke magana a kai,
inda suka rungumi amfani da wannan da ake siyarwa a shaguna wanda wannan lallen hade-hade ne kawai na wasu sinadaran da har illatarwa suke yi. Kusan abin da suke kallon maccen da take yin lallen gargajiya tamkar bakauyiya.
A yau wannan shafin ya dukufa wajen farfado da asalin maganin da muke da shi tun a zamanin da wanda aka dauki lokaci mai tsawo ana cin moriyarsu, amma sai gashi a yanzu an fara mantawa da su, shi ya sa wasu cututtukan zamani suka gagari magani.
-Na farko dai darajar mace mai yin lalle ba ta daya da wacce ba ta yi ko farin jinin su da tagomashin su ba zai zamo daya ba.
-Lalle kariya ce daga aljannu dalili a nan shi ne, akwai miyagun aljanun da suka tsani ganyen lalle.
-Lalle na karya sihiri a jikin mace, dan haka sai a nemi ciyawar aniya makomiya a dake tare da ganyen lalle a ringa shafawa.
-Lalle kariya ce daga cututtuka masu dama musamman na fata.
Comments
Post a Comment