Main menu

Pages

AMFANIN MAN KWAKWA GA LAFIYAR JIKI


 


AMFANIN MANKWAKWA  GA LAFIYA


Man kwakwa yana da amfani sosai, kuma ana amfani da shi ta hanyoyi da dama domin bukatar mu da ta iyalan mu. Ga wasu daga cikin amfanin sa kamar haka:


 1. Amfani da shi domin yin girki, soya miya ne ko kuma soye-soyen kayan kwalam da ma kwalashe.


 2. Zubawa a cikin abinci ko kuma cikin lemon domin karawa jiki kuzari da karfi.


 3. Shafawa a jiki domin fata tayi laushi da santsi, musamman ga masu bushewar fata da kuma gautsi.


4. Ina "yammata masu shafa hoda fankeke (foundation powder) da aye shado (eye shadow)? Idan kun tashi wanke fuska ku shafa man kwakwa kafin ku wanke fuskar ku, domin sabulu bai cika wanke irin wannan kwalliyar da kyau ba. Amma idan aka shafa man kwakwa fuskar tana saurin wankuwa kuma tayi kyau, ko baki shafa mai ba za ki ga tana sheki da kyalli.


5. Shafawa jajirai a al’aurar su don gudun samun kuraje a wajen, ko kuma idan sun sami kuraje a wajen ana iya shafa musu man kwakwa don wajen ya yi saurin warkewa. 


6. Idan kina da nankarwa sai ki ringa shafa man kwakwa a wajen, za kiga ta baje ko kuma ta ragu, amma sai kin lizimci sahafawa a wajen. Ko kuma idan mace tana da ciki idan tana gudun kada ta sami nankarwa sai ta ringa shafa man kwakwa a cikin ta to ba za ta fito mata ba da izinin Allah.


7. Ina mata masu fama da karyewar gashi da rashin sheki? To ga maganin matsalar ki. Ki ringa shafa man kwakwa a kan ki domin gashin ki ya yi laushi ko kuma ya daina karyewa. Kuma yana kara tsawo da cikar gashi. 


8. Wasu matan suna yin sabulun wankan su da kan su, kamar sabulun salo da sauran su. Kina iya zuba man kwakwa a cikin sabulun saboda wasu sabulun idan kin yi amfani da su za ki ga suna busar da jiki, amma idan a gida ki ke hadawa to sai ki zuba man kwakwa a ciki. idan ma kin siyo na kanti kina iya zuba man kwakwar a ciki, wato ki daka sabulun ki zuba man a ciki sannan ki cura ko ki mulmula yadda kike so. 


9. Idan leban ki yana yawan fashewa to ki samu man kwakwa ki ringa shafawa a leban musamman lokacin sanyi. Idan ba kya son ki ringa shafa man kwakwar shi kadai kina iya zuba shi a cikin wani man ki kwaba ki ringa shafawa a leben. 


10. Idan kina fama da kyasbi to ki mayar da man kwakwa ya zama man shafawar ki a ko da yushe.


11. Mata masu fama da kwarkwata har ma da wasu mazan ki ringa shafa man kwakwa a gashin ko kuma ki hada shi da ruwan khal ki ringa shafawa a gashin, wannan magani ne sosai.


12. Mata masu shayarwa wani lokacin zaki ga kan mamanki ya tsatstsage wani lokacin ma har da jini, to ki ringa shafa man kwakwa akai-akai. Haka kuma mace mai shayarwa tana iya shan cokali 3-4 na man kwakwar domin kara samuwar ruwan mama.


13. Man kwakwa yana sa ciwo ya yi saurin warkewa, yana sa nan da nan wurin ya kame ya kuma bushe.


14. Idan kina fama da mura sai ki ringa zuba cokali 2 zuwa 3 a cikin ruwan shayi domin samun saukin murar, haka ma idan kina fama da ciwon makogaro shi ma sai ki zuba cokali uku a cikin ruwa mai dumi ki ringa sha. 


15. Idan kina fama da kurajen fuska wato (pimples) to ki dimanci shafa man kwakwa za ki ga sun tafi, har da wannan baki-bakin zaki ga sun baje.


16. Idan tukwanen ki ko kasake ko kuma murahu sun yi tsatsa kina iya amfani da man kwakwa domin ganin tsatsar ta tafi.


17. Maganin faso, ki hada man kwakwa da dan gishiri kadan sai ki ringa shafawa a kafar, za kiga bushashshiyar fatar tana cirewa da kan ta, kafar kuma tana yin laushi.


18. Ki yi amfani da man kwakwa domin rage kaikayin farankama ko kuma cizon sauro.


Comments