Main menu

Pages



 JAN HANKALI AKAN SALLAR ASUBAH SALLAH ITACE MAFI ALKHAIRI FIYE DA BACCI. MU RAGE BACCCI DON MU RIBAN TA DA GOBEN MU


1. Bacci amsawr kiran Zuciyane.

Sallah kuwa amsawa kiran Ubangiji ne.


2. Shi Bacci mutuwane.

Sallah kuwa Rayuwace.


3. Shi Bacci hutune na Gangar jiki.

Sallah kuwa hutune na Ruhi.


4. Shi Bacci da Mumini da Kafiri duk suna yinsa.

Sallah kuwa Mumini ne kadai yake yinta.


Masu tashi lokacin hudowar Alfijir sun rabauta, Fuskarsu kuma ta haskaka Goshinsu kuma shima yayi haske da kyalli, lokacinsu kuma yayi Albarka. Idan kana cikinsu to kagodewa Allah (s.w.t.) daya fifitak ba idan kuma baka cikinsu to Karoqi Allah (s.w.t) yasakaka acikinsu.


Menene yafi Alfijir kyau?

Farillarsa (Sallar Asuba) zata sakaka acikin kulawar Ubangiji da kariyarsa, 


Sunnarsa: (Raka'ataylfajri) itace tafi Duniya da abinda yake cikinta.


Sallarsa (kamar yadda Malaman tafsiri suka fassara wannan aya ta 78 Suratul - Isra'i وقرآن الفجر ana nufin Sallar Asubahi).



Ita Sallar Asubahi Mala'iku masu duty safe da masu duty dare duka suna halartota. (Domin alokacin suke handing over na duty su acikin wannan Duniya tamu).



Ya kai Dan'uwa/Yar uwa Mai girma kasani cewa : Duk wanda yarayu akan wani aiki to akansa zai mutu, wanda kuma yamutu akan wani aiki to akansa za'a tashe shi.



Idan kakaranta wannan Saqo kuma kayi aiki dashi to kasami Ladan aikin ka idan kuma katurawa wasu suma sukayi aiki dashi to Ladanka zai nunku awurin Allah (s.w.t) In Allah yaso.



Kada kaboye Ilimi, Kabayyana shi zaka sami Kyakkyawan Sak amako.

Kuyi Murna yaku masu Sallar Asubahi acikin Lokacin ta kuma acikin Jam'i. Wallahu Aalam.

Comments