KU KIYAYI BARAWON WATAN RAMADAN
BARAWO NA FARKO:
Television: barawo ne me hadari Wanda yakan bata azumin wasu ya kuma rage ladan azumin wasu bisa shirye-shirye da yake bijuro masu dashi, da sunan dauke kewa, nishadi da makamantan su
BARAWO NA BIYU
KASUWANNI: Kasuwa tana sace dukiya da lokaci ba tare da an farga ba. Sabo da haka yi kokari ka killace naka
BARAWO NA UKU
HIRA: Hirarraki na sace mana mafiya yawan lokutan mu ta yadda muke kasa ribatar karshen dare da Nafilfilu da Istigfari
BARAWO NA HUDU
MADAFA: (kitchen) Mata da dama na daukan lokaci mai yawa waje dafe-dafe na abinci daban-daban don launanawa baki dandano mai yawa, kuma karshe kaga ana zubar da abinci a bola sakamakon yawa na abincin.
BARAWO NA BIYAR
WAYAR HANNU: Doguwar tattaunawa, wadda ta tattaro gulmace-gulmace, Annamimanci, yada sirrin mutane, ance-ance.
Chats marar ma'ana marar amfani.
Duk motsi kadan latsa waya (minti 2, 3, 5, sama ko kasa da haka)
BARAWO NA SHIDA
ROWA: tana haramta maka ladan sadaqa da kyauta (wadan da suke hana shiga wuta cikin rahama ta Ubangiji musamman a RAMADAN )
BARAWO NA BAKWAI
MAJLISI/DABA: Wurin Zaman mutane wadda ba ambaton Allah cikin sa, tabbas akwai nadamar halar tar irin wadannan wurare a ranar ALQIYAMA
Hanyoyin na gamayya da sadarwa dayawa in ka kaurace musu kafi samun yardar Allah cikin sauki.
Comments
Post a Comment