GUZIRIN WATAN RAMADHAN
An tambayi wani Malami cewa: Wace nasiha za kai mana domin taryar watan Ramadhana? Sai yace: Mafi alkhairin abinda zaka taryi watan Ramadhana da shi shine "yawaita Istigfari" domin kuwa zunubai kan hana bawa samun dacewa.
Bawa bazai gushe ba yana lazimtar istigfari face sai ya tsarkaka, idan mai rauni ne zai karfafa, idan mara lafiya ne zai samu lafiya,
Idan yana cikin kunci zai samu waraka, Idan kuma yana cikin rudani ne zai samu shiriya, idan yana cikin tashintashina zai samu nutsuwa.
Kuma lallai Istigfari shine amincin da ya rage mana bayan Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.
Duk wanda ya siffantu da wannan siffar ta (siffar istigfari) Allah zai yassare masa samun arziki, ya saukaka masa al'amuransa, ya kuma kiyaye masa sha'anoninsa da karfin sa.
Sayyidina Umar ibn Khaddab yana cewa : Da ace tsawa za ta fado daga sama to baza ta fadawa mai istigfari ba.
Duk wannan yana nuna mana tsananin muhimmancin yin istigfari.
Ya Allah muna rokonka ka dauwamar da harshenmu akan anbatonka,
Ya Allah ka gafarta mana zunubanmu wanda muka sani da wanda ba mu sani ba.
Ya Allah mun tuba
ASTAGFIRULLAHA WA ATUBU ILAIHI.
Comments
Post a Comment