MAGANIN CIWON HANTA.
Ciwon hanta ya zama ruwan dare Inda yake kara yaduwa a tsakanin Al'ummah.
Ga wata fa'ida wanda masu fama da wannan ciwon zasu iya jarrabawa domin samun waraka daga lalurar cikin nufin Allah.
Hanya Ta Farko 1
1.Ganyen Zugale busashshe
2. Yayan Baure ko garin yayan busashshe.
Yadda Za a Hada
Sai a hade waje guda a dake su suyi laushi, mai fama da Matsalar ya rika shan karamin chokali a nono ko kuma madara ta ruwa ko kunu sau 2 a rana.
Hanya Ta Biyu 2
MAGANIN HEPATITIS A, B & C (CIWON HANTA)
ALAMUN CIWON HANTA
Akwai matsanancin ciwon kai da ciwon malariya da typhoid akai-akai.
・ Haka zakaji ciwon jiki da rashin karfin jiki, ciwon ciki mai tsanani.
・ Yawan haraswa dakuma tashin zuciya koda ruwa kasha.
・ Ido yakanyi yellow, da rashin dandano a baki, fitsari ya koma yellow, ko matsananci zazzabi da jin sanyi, bayan gidan mutum yakan koma kalan kasa.
MAGANINTA
1. A samu garin habba cokali 10
2. Garin Sidir cokali 5
3. Garin tin cokali 5
4. Garin bawon kankana cokali 10
5. Garin Citta cokali 1
6. Garin tafarnuwa cokali 1
7. Garin Hidal cokali 5
8. Garin zogale cokali 3
9. Garin Yansun da raihan da kusdul hindi cokali 6
Sai a hadasu waje daya a samu Zuma lita biyu mai kyau sai a zuba ciki a juya ya hadu sosai sai a dinga shan cokali uku sau uku a rana.
MAGANIN YAWAN MANTUWA,.DA KAIFIN KWAKWALWA.
Domin magance yawan mantuwa,da kuma karawa kwakwalwa karfi,ga wata fa'ida sai a jarraba kuma insha Allah za a samu nasara.
1. Garin ik'lil jabal (rosemary)
2. Na'a Na'a (mint leaves)
3. Girfa (cinnamon)
YADDA ZAA HADA
Za a samu kowanne magani da muka ambata garinsa, kmar chokali 5 kowanne sai a hade su waje guda a rika diban chokali 1 a tafasa kamar shayi da ruwa kofi 2 asha kofi daya safe daya yamma, za a iya sa Zuma ko sukari idan za a sha.
Dukkan wanda ya jarraba wannan fa'ida zaiga banbanci insha Allah.
Comments
Post a Comment