DALILAN DA YASA SUKE HASSADA DA MINISTA PANTAMI KENAN
√ Shine Dan Afrika na farko da ya taba zama shugaban tsangayar koyon rubutun musulunci a Jami'ar Madina a shekarar 2014.
√ A cikin kasa ga shekaru uku ya nuna irin bajintar sa inda ya samu kyaututtukan girmamawa guda dari da goma (110) a ciki da wajen Nijeriya.
√ Haka kuma ya samu kyautar mutum mai kwazon daukaka ko samar da cigaban harkar sadarwa ta zamani wato ICT Promoter a turance a shekarar 2017 a Birnin London.
Sunan wannan bawan Allah shine: Sheikh Dakta Isah Ali ibrahim Pantami
Ya samu Digiri da shaidar karatu kamar haka:
> Digirin farko wato Bsc akan hakar Na'ura mai kwakwalwa (Bsc Computer) a Jami'ar ATBU dake garin Bauchi
> Yayi Digiri na biyu wato Msc a turance a fannin ilimin Na'ura mai Kwakwalwa a Jami'ar ta ATBU (Msc Computer)
> Ya samu takardar shaidar MBA Technology a Jami'ar ATBU dake Bauchi
> Ya samu Digirin Digirgir wato Ph'D Oil and Gas Computing a kasar England
> Ya samu Digiri a fannin samar da sauye-sauye a fannin yanar gizo wato Digital Transformation a Jami'ar Harvard
> Ya samu shaidar strategic innovation a MIT, dake kasar Amurka (USA)
> Ya samu takardar shaidar Management a Jami'ar Cambridge, dake USA
> Ya koyar a Jami'ar ATBU dake Bauchi
> Ya zama babban Darakta na hukumar NITDA a Nijeriya
> Ya zama Ministan sadarwa da kuma tsare-tsaren tattalin arziki na zamani wato Communication and Digital Economy a Turance
> Babban mahaddacin Qur'ani ne
> Babban mai wa'azi da fassarar alkur'ani ne
Muna Addu'ar Allah ya yi maka jagora akan makiyanka na fili dana boye Malam
Comments
Post a Comment