Main menu

Pages

ABBWN DA KE KAWO MA MACE CIWON MARA, DA HANYAR DA ZA A BI DON MAGANCE SU

 


MAGANIN CIWON MARA


Abubuwa masu saka mace ciwon mara suna da yawa to amma wadanda sukafi tasiri a ciki sune lokacin al'ada, ko kuma mace me ciwon sanyi, akwai kuma wadanda suke yin maganin tazarar haifuwa, wadannan kusan duka sune dalilin  ciwon mara ga mace,




 LOKACIN AL'ADA

A lokacin da jinin al'ada zaizo yana samun datti wanda hakan zai sashi daskarewa kafin yabar wajen sai ya tsinke ya zama ruwa, wata kuma maniyi da yake daskarewa shine yake hana jinin zuwa da wuri, hakan zaisa mara ta rinka ciwo amma kuma idan ana shan maganin wanke mara zaizo cikin sauki, ko garin hulba kika tafasa kikaha ruwan yana bude mahaifa cikin sauki zaizo.





CIWON SANYI

Akwai ciwon sanyi me saka ciwon mara wanda take kullewa ana iya samun maganin sanyi na gargajiya wanda yake da nasaba da hakan, amma kafin nan aje asibiti domin a tabbatar da ciwon sanyin ne ya jawo ciwon mara din.






TAZARAR HAIFUWA

An tabbatar kowanne irin maganin bature da zai dakatar da samun ciki zai iya saka ciwon mara ko kuma wasan al'ada, dalili kuwa da yawa magungunan mahaifa suke toshewa maniyi bazai shigaba, 



kafin yazo kuwa dole ya bada wahala wajen kullewar mara, wani kuma yana saka cuta ajikin mahaifar wanda kusan kullum mace tana fama da ciwon mara, domin samun waraka ana iya shan magungunan wankin mara ko kuma aje asibiti domin tabbatarwa akan matsalar.

Comments