YANDA AKE DAFA KAZAR AMARYA
Tsarin da mata da yawa suke bi wajen dafa kazar amare da yawa kuskure ne kuma sihirine wannan shine.
Kuskure ne ace sai an zuba rubutun ayoyin alqur'ani aciki ko kuma ace mace daya ita zataci wannan kazar ko kuma ace dole sai ranar laraba duk wadannan ba sune sukesa namiji ya makalewa mace ba kuma ita wannan kazar ana yinta saboda tana tabbatarda ni'ima a jikin mace sannan gaban mace ya ciko kuma tana saka mace tayi dandano sosai ta yanda mijinta kowanne lokaci zaiso ya sadu da ita haka kuma tana saka mace ta zama me sha'awa amma maganar mallakar miji wannan ba gaskiya bane...
TA YAYA AKE DAFA KAZAR?
Ki samu ridi danye ki daka shi ya zama gari saiki samu harzar kabewa ki zuba mata ruwan zafi ki barta ta jiku sai ki tace ruwan saiki zuba wannan garin ridin sannan ki daka minannas ki zuba garinsa aciki to wannan ruwan shine zaki dafa kazar aciki
Amma ki samu budurwar kaza bayan kin gyarata kin cire kayan hadin saiki zuba idan da hali ki samu farin gadali ki daka ki zuba aciki zaki iya zuba kayan miya yanda kikeso ki dafata ta dafu sosai sannan ki sauke ki cinyeta gaba daya har miyar wannan itace kazar amare kuma kowacce mace zata iya kuma zatayi idan saura kwana hudu a sadu da ita...
kashin farko kenan mu hadu a wani darasin domin jin wani salon dafa kazar
Comments
Post a Comment