GYARAN GASHI
hanyoyi guda biyu da kowacce mace zatabi ta samu tsayin gashi da laushi da baki duka ba tareda tayi amfanida maganin bature ba
Abu na farko shine amfani da tafarnuwa da man zaitun yanda zakiyi saiki samu tafarnuwan da dan yawa kamar sama da goma saiki baresu ki yanyanka sannan ki jikasu da man zaitun saiki bari yayi kwana uku ajike saiki soya ki ajiye kina shafawa akai bayan sa'a daya (1hour) a wanke.
Sai kuma na biyu shine amfani da man amla da man kwakwa da zuma yanda akeyi shine zaki zuba man amla kadan zuma itama idan amla ya zama cokali 4 to zuma ya zama cokali 2 man kwakwa shima cokali 2 sai ki zuba a ruwan zafi shi kuma kamar cokali 4 a gauraya kamar idan za'ayi shampoo sai ashafa akai bayan mintuna talatin (30minutes) shikenan sai kiyi shampoo dinki.
Comments
Post a Comment