Gareku Masu Dora Pic a Social media
Victim din ta fara da bada Labarin ne kamar haka;
Salam zan baki labarin abinda yafaru dani,
don girman Allah ki tura ma "yan uwa sabod bana fata hakan ya faru da wata, ki yada shi domin ya zama darasi ga masu aikata hakan,
Lokacin dana bude Facebook da WhatsApp pic din 'ya tace akan dp dina, akwai wata data turoman Friend request nayi accept dinta, muna chat sosai da ita har a WhatsApp, munsaba tana yawan tambayana pic din Afra nikuma sai na bata indai nasaka pic a dp dina sai tayi comment.
Wallahi ko sati ba muyi da haduwa ba, Afra tafara zazzabi mai zafi muna zuwa hospital doctor yace Jini za a qara mata tun daga lkcn bata kwana uku sai tayi kuma da munje Dr zaice Jini, An qarama Afra jini yakai Leda 15, a wata daya randa muka dauki azumin farko yaqara tashi shine Dr yacema mijina gsky matsalan "yarka bana hospital bane, yayi mana hanya mukaje Islamic Chemist
muna zuwa Malamin yace wlhy Aljanace ajikin yarinyarku ita take kwashe mata jini Nida mijina hankalinmu yayi masifar tashi, agabana yafara yimata Ruqiyya ko minti biyar ba'aciba yarinya tafara chanja kala, tana wani irin Gunji kamar ba mutunba,
Malamin yafara yimata tambaya akan tafita ajikinta, sai tayi magana da wani murya ita bazata fita ba sbd tana sonta tun randa tafara ganinta, Malamin yace a ina kika ganta, tace a Facebook mamanta tasata akan dp dinta, naji ina sonta shine tayi mai bayani tun farkon haduwar mu da ita.
Mijina ya fara fada, Malamin ya bashi hkr, Wallahi iya firgita na firgida sosai, dakyar da roqon Allah tace zata bar jikinta, yahada mana magunguna, yace mudage da addu'a sosai akanta
Tunda muka fito wlhy baiceman komiba, harmuka koma gida muna shiga yace in shirya kayana kamun yadawo, jikina yayi sanyi, yana dawowa yabani takardan Saki daya, yace nabashi "yarsa ya ansheta ya kaima Abokiyar zamana,
Wallahi yau kwanana Hudu kenan agidan mu kowa ya tsaneni, ina cikin tashin hankali wallahi nayi dana sanin bude Facebook arayuwata,
Inabaran Addu'arku nida yata Afra 🙏
Wannan shine Labarin Maman Afrah a takaice, don haka wannan ya zamo iznah ga masu sanya pic dinsu ko na 'ya'yansu a social media saboda rashin mafadi.
Ina mamaki kwarai bansan me wasu suka dauki wannan dandali ba, wasu ma duk abinda suke sai sun rubuta a status ko a dauki hoton ayi ta dorawa saboda qauyanci.
Comments
Post a Comment