Main menu

Pages

HUKUNCIN ALLURAR JIJIYA DA TA DAMTSE GA MAI AZUMI

 



HUKUNCIN ALLURAR JIJIYA DA TA DAMTSE KO GABBAI GA MAI AZUMI



Menene hukuncin amfani da allurar da ake yinta a jijiya, da wacce ake yi a damtse ko a gabbai ga mai azumi, menene kuma banbacinsu?




 Ingantaccen magana shi ne: Gaba dayansu biyun (ta jijiya da ta damtse) basa bata azumi, wanda kawai take bata azumi itace allurar da ake sanya mata abinci. Haka kuma daukan jini don bincike, shima azumi baya karyewa da shi, saboda akwai banbanci tsakaninsu da yin qaho. 



Amma shi kuma kaho da wanda ya yi shi da wanda aka yi masa dukkansu azuminsu ya karye, a maganar maluma da ta fi inganci, wannan kuma saboda fadinsa (صلى الله عليه وسلم):


«أَفْطَرَ الحَاجِمُ وَالمَحْجُومُ».


Ma’ana: “Da mai Kaho da wanda aka yi masa Kahon azuminsu ya lalace“.

Comments