HUKUNCIN AMFANI DA NA’URAR FESA ISKA A CIKIN BAKI (INHALER) DON MATSANANCIN BUKATA HAKA, A WAJEN MAI AZUMI:
Menene hukuncin amfani da na’urar maganin da ake fesa iska a cikin baki (inhaler), ga mai azumi a cikin yini (wato: da rana), ga mai ciwon quncin qirji da wahalar yin numfashi (Asma)?
Hukuncinsa shine halacci; idan har lalura ta buqatar da mutum zuwa ga hakan, saboda fadin Allah mabuwayi da daukaka a cikin “suratul an’aam”:
ﭽ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭼ الأنعام: ١١٩
Ma’ana: “Kuma ya muku dalla-dallan abubuwan da ya haramta su akanku, saidai wanda lalura ta buqatar da ku zuwa gare shi“, [An’aam: 119].
Kuma saboda kasancewarsa baya kama da ci da sha, sai ya yi kama da jinin mutum da ake dauka don aunawa ko bincike, ko kamar allurar da ba a sanya abinci a cikinta ba.
Comments
Post a Comment