HUKUNCIN YIN AMFANI DA MAKILIN, DA MADIGI
Menene hukuncin amfani da makilin din goge haqora, da kuma madigin kunne (magani), dana hanci, dana ido, ga mai azumi? Kuma idan mai azumi ya ji dandanonsu a cikin maqogoronsa me zai aikata?
Tsaftace haqora da makilin baya karya azumin mai azumi, saboda hukuncinsa kamar yin aswaki ne, Saidai kuma wajibi ne akansa ya kiyaye silalewan wani abu zuwa cikinsa, Amma inda wani abu zai rinjaye shi ya shiga cikin cikinsa ba tare da nufi ba to babu ramuko akansa.
Haka maganin digawa a ido da kunne azumi baya karyewa in an diga su a zancen da yafi inganci daga zantukan maluma guda biyu, Saidai kuma in har ya ji dandanon abubuwan da ya diga a makogoronsa to ya rama wannan azumin yafi tsentseni a gare shi, tare da cewa yin hakan ba wajibi ba ne akansa, saboda kasancewar ido da hanci ba kafofi ne na shigar da abinci da abin sha ba.
Amma maganin da ake digawa ta hanci to shi kam baya halatta; saboda kasancewar hanci mashiga ne na abinci, don haka ne Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ke cewa:
«وَبَالِغْ فِي الِاسْتِنْشَاقِ إِلَّا أَنْ تَكُونَ صَائِمًا».
Ma’ana: “Kuma ka kai maqura wajen shaqar ruwa a hanci saidai in ka kasance mai azumi”. Kuma wajibi ne ga mutumin da ya aikata hakan ya rama azumi, saboda wannan hadisin da wadanda suke da ma’ana irin tasa, matukar ya ji dandanon abun da ya diga a cikin makogoron nasa, Allah shi ne majibincin dacewa.
Comments
Post a Comment