HUKUNCE HUKUNCEN JINI GA MAI AZUMI
Mata da sukeyin ɓari (miscarriage) basa fita daga cikin ɗayan hali guda biyu; imma ya kasance lokacin da tayi ɓarin cikin ya girma (an halicce shi) ko kuma ya zama ƙaramine ba ahalicceshi, to meye hukuncin azuminta a irin wannan lokacin da kuma ranakun da jinin zai cigaba da zuwa mata??
Idan har ya kasance cikin ƙaramine ba'a halicce shi ba, to awannan lokacin jinin da zai zo mata ba jinine na ɓiki (Nifasi) ba, jinine na ciwo, dan haka zatayi sallah da azumi, amma idan ya kasance an halicce shi to jinin jinine na Nifasi baya halasta tayi sallah da azumi.
Qa'idar da zata riƙe a wannan mas'alar itace, idan an halicci jaririn to jinine na Nifasi idan kuma ba'a halicce shi ba to ba jinin Nifasi bane, idan kuma jini na Nifasi ne to baya halasta ayi sallah da azumi, idan kuma ba na Nifasi bane to za'ayi sallah da azumi.
NOTE
Cikin da ya kai wata huɗu shine wanda aka halicci jaririn, wanda yake ƙasa da wata huɗu to ba'a halicce shi ba, idan mace tayi miscarriage awannan lokacin zata cigaba da Sallah da azumi.
Comments
Post a Comment