"Duk Dan Nijeriya Da Aka Yi Garkuwa Da Shi Ya Biya Kudin Fansa, Zai Fuskanci Hukuncin Shekaru 15 A Gidan Yari"
Majalisar Dattawan Nijeriya ta gabatar da sabon kudirin doka akan cewa duk wani 'dan Nigeria da aka yi garkuwa da shi, ya biya kudin fansa don ya kubutar da rayuwarsa, to zai fuskanci hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari sakamakon biyan kudin fansa da ya yi.
Da zarar majalisa da shugaban kasa sun amince da wannan sabon kudirin doka, idan an yi garkuwa da kai kana da zabi biyu:
1- ko dai a hakura da kai masu garkuwan su kashe kayi bankwana da duniya
2- ko kuma ka biya kudin fansa ka bar hannun masu garkuwa da mutanen ka dawo gida hukuma ta kamaka a kaika kotu ka tafi gidan yari shekaru 15
Wannan shine halin tsaka mai wuya kenan gare mu talakawan Nijeriya, gaba zakanya, baya damisa.
'Yan uwa shin kuna goyon bayan wannan doka a tabbatar da ita?
Yaa Allah Ka bamu mafita na alheri Ameen
Comments
Post a Comment