HUKUNCIN AUREN KASHE WUTA
Hukuncin mutumin da ya saki matarsa saki uku daga baya shi da ita suka je suka nemi wani da yarjejeniyar auren sati 1, kuma shi tsohon mijin shi ya biya sadakin, bayan satin sai tsohon mijinta ya mayar da ita?
Idan mutum ya saki matarsa saki uku, to ba ta halasta a gare shi har sai ta auri waninsa, aure na buqata ba da nufin halastawa mijinta na farko ita ba, kuma dole sai ya zama mijin na biyu da ta aura ya yi kwanciyar aure da ita kamar yadda nassoshin Shari'a suka tabatar.
Sannan dole ne ya zama ba haɗa baki mijinta na farko da na biyu suka yi da nufin ya aure ta su yi zaman aure zuwa na wani lokaci sai ya sake ta, shi kuma mijinta na farko ya mayar da ita ba. Idan aka samu wannan sharaɗi a auren ta da miji na biyu, to dukkan malamai sun ce wannan aure ɓatacce ne kuma haramun ne. Irin wannan aure shi ne malamai suke ce masa auren halastawa miji na farko, wato (Nikáhut Tahleel), irin wannan aure ɓatacce ne kuma haramtacce ne bisa fahimtar dukkan malamai.
Kuma irin wannan aure malamai sun ce ba ya halasta wa miji na farko matar, haka shi ma miji na biyun ba ta zama halas a gare shi ba ko da kuwa bayan an qulla auren ne, dukkan su biyun ba ta halasta ga ko ɗayansu ba, saboda aure ne ɓatacce kuma haramtacce. Har Manzon Allah ﷺ ma ya tsine wa mai yin auren halasta ma wani, da kuma wanda aka halasta mawa ɗin, wato miji na farko da na biyun, kamar yadda Abu Dáwud ya ruwaito a hadisi mai lamba: (2076).
Saboda haka ƴar uwa ya zama lazimi a kan wannan mata da wannan miji su rabu, saboda su ba ma'aurata ba ne a Shar'ance, aurensu ɓatacce ne kuma haramtacce, su yi nadama da tuba zuwa ga Allah saboda yin wannan babban laifi.
Amma in da a ce ita matar da aka saka saki uku, ita ce ta nemi wani ya aure ta da nufin in ta yi auren ta kashe don ta koma wurin mijinta na farko, ba tare da sanin miji na farko ba, ba kuma tare da sanin miji na biyu ba, to wannan ko da ta yi sanadin mutuwar auren don ta koma wurin mijinta na farko babu laifi, matuqar wannan mijin na biyu da ta aura ya yi kwanciyar aure da ita. Saboda a nan miji na farko ba shi ya nemi a halasta masa ba, shi ma miji na biyun bai yi hakan da nufin halasta wa mijin farkon can ba.
Duba Almugniy (7/180, 181) domin qarin bayani.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Comments
Post a Comment