Main menu

Pages

HUKUNCIN SANYA TURARE GA MATA

 





 HUKUNCIN SANYA TURARE GA MATA



Hukuncin Sanya TURARE ga mata a adinin MUSULUNCI

        

Daga Ubaidu Yace :

"Lallai Abu Hurairata (Allah yakara masa Yarda) ya hadu da wata mãta wacce ta sanya Turare, Sai Yace Mata : Ina kikeson zuwa ne haka Baiwar Allah?

Sai mãtar tace : Masallaci zanje.


Sai Yace : Saboda zaki Masallacin ne kika sanya Turare? Sai mãtar tace : eh.

Sai Abu Hurairata Yace : Lallai ni nãji Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Yace : "Duk mãtar da ta sanya turare tafita da nufin zuwa Masallaci, to Allah mai girma da daukaka ba zai karbi sallarta ba har sai ta dawo ta yi wanka Irin wankanta na Janaba."



{Ibn mãjah ne ya ruwaito shi acikin KITABUL FITAN babin Fitnatun Nisã'i (4002)} SHEIKH NASIRUDDEEN ALBÂNY Yace : Hadisin mai kyau ne Kuma Ingantacce ne.



Malamin Addinin Islama NASIRUDDEEN ALBÂNY (Allah yayi masa rahama) yayi ta'aliqi akan haka, YAKE kara cewa :



" Idan har (sanya turare sbd) zuwa Masallaci yazama Harãmun, to ya (ake tunanin) hukuncinsa zai Kasance akan (wacce ta) sanya shi sbd zuwa Kasuwa, Titi da kuma hanyoyi ?

Babu makawa yin hakan ya fi tsananin haramci kuma ya fi girma wajan sa6o!!!


IMÂM AL-HAITHAMY yana fada acikin (Az-awãjir 36/2) "Lallai fitar mace da zatayi tana mai sanya Turare kuma tana mai kwalliya, yana daga cikin MANYAN LAIFUFFUKA kuma ko da mijinta ne yayi Mata izini, kuma duk wadannan Hadisan (wadan da suke nuna haramcin sanya turare ga mace idan zata fita waje) baki dayansu sun shafi gaba dayan lokuta ne. ".



To amma wasu sai duke ganin kenan banda Matan da basu da aure wannan haramcin ya shafa. Saboda dukkan hadisan Suna nagane akan Matan aure. To Allah dai Shine magi sani.



[Mukhtasar Kitãbu jalbãb Al-mar'atul muslimah (shafi na 44)]. YA ALLAH KA AZURTAMU DA MAZA NAGARI, KUMA KA AZURTA MAZAN DA MATA NAGARI.


Wallahu A'alam. 


Comments