SIRRIN LEMON TSAMI
Ashe Lemon tsami yana da illa ga Farjin Mata:
Da Mata Sunsan wannan Dakuwa farji Ya Huta Da wahala
"Lemon tsami yana da sinadarin ACID da ke mataki na biyu cikin sha hudu 2/14, haka ita ma al'aurar mata na tsakanin mataki na 3.8/14 zuwa 4.5/14," in ji kwararriya Likita
Al'aurar 'ya mace wuri ne mai matukar haɗari da ke bukatar kulawa ta musamman saboda irin tsarin halittar da aka yi mata.
Wuri ne mai daukar cuta cikin hanzari, sannan ya yaɗa ta cikin sauki.
Don haka a baya iyaye da kakakanni ke cewa a yi amfani da wasu abubuwa irinsu lemon tsami domin tsafta ce ta daga wari da kuma kamuwa da cutuka.
Sai dai da zuwan kimiyya an samar da wasu sinadaren da akan iya wannan aiki da su ba tare da haifar da illa ga al'aurar mata ba ko kuma mahaifarsu, kamar yadda Dakta Fatima Abdulahi wata kwararriya kan sha'anin cutukan mata da ke aiki da kungiyar Marie Stopes International a birnin tarayyar Abuja.
Dr Fatima Abdullahi
Alakar lemon tsami da al'aurar mata
Dakta fatima ta ce a kimiyyance a jikin ko wanne abu akwai sinadarai irin su ACID da ALKALINE kuma akwai iya matakan da ake bukatarsu a jiki. Idan suka yi yawa za su haifar da matsala haka zalika in suka yi karanci.
"Lemon tsami yana da sinadarin ACID da ke mataki na biyu cikin sha hudu 2/14, haka ita ma al'aurar mata na tsakakin mataki na 3.8/14 zuwa 4.5/14," in ji kwararriyar.
Zaman al'aurar mata a wannan mataki shi ne take da kariya babu wata cuta da za ta iya farmata nan da nan, a cewarta.
(Za mu fassara ACID da kalmar kaifi) Yawan sinadari mai kaifi da ke cikin lemon tsami ya fi na al'aura karfi, don haka idan ana yawan amfani da lemon tsami a al'aurar zai haifar mata da illoli masu yawa.
Illar lemon tsami ga al'aura: 12
Saboda sinadarin lemon ya fi karfi, zai iya sauya tsarin halittar al'aurar ya mayar da ita mai rauni, in kuma ta zama mai rauni za ta iya daukar cutuka masu yaduwa ta hanyar jima'i cikin sauri, in ji likitar.
Yawan amfani da lemon tsamin zai iya yayyanka bututun mahaifa wanda hakan ka iya kai wa ga kamuwa da kansar mahaifa.
In kuma aka samu rauni a al'aura hakan na iya kai wa ga shigar kwayar cutar HIV, wadda ita dama neman wajen da yake da rauni ta ke yi domin ta samu wajen zama daram.
Masana kimiyya sun gano cewa al'aurar mace wuri ne da yake tsaftace kan shi da kan shi lokaci zuwa lokaci.
Shan Lemon tsami na yi wa mata illa kamar yadda ake cewa yana yi wa maza?:
Kwararriyar likitar kan sha'anin cutukan mata ta ce babu wata illa da lemon tsami ya ke yi wa mata dan sun sha.
A shekarun baya akan ce idan mace na yawan shan lemon tsami yana kawar mata da budurcinta, amma ta ce sam wannan zance ba shi da wani tushe a kimiyyance.
"Lemon tsami ya kan hana wasu cutuka yin tasiri a jiki, yakan gyara fata da ƙara karfin garkuwar jiki a wani lokacin kuma ya kan zama sinadarin Vitamin C a jiki" in ji ta.
Shawara game da amfani da lemon tsami:
Lemon tsami yana kashe warin jiki irin na su hammata da kuma al'aura ga duka jinsin mata da maza.
Amma ba a fiye son a yi amfani da lemo zalla ba, an fi son a sirka shi da ruwa domin kashe kaifinsa don gujewa kamuwa da abubuwan da muka lissafa a baya.
Dakta Fatima ta ce akwai wani bincike kan amfani da lemon tsami da aka yi a turai, da ya nuna matan da ke amfani da zallan lemon stami ga farjinsu sun kamu da cutuka masu yawa.
A wajen tsaftace al'aura an fi son a yi amfani da ruwa mai dan dumi, a kula, mai zafi sosai zai iya kai wa ga wasu cutukan na daban.
Comments
Post a Comment