MACE MAI NEMAN HAIHUWA
Idan kina neman haihuwa ko kin dade baki haihu ba to Dr Mubarak mjb yace ki jarraba wayan nan magungunan da Allah yayi masa baiwarsu SIRRI NA DAYA
Kisami garin hurmul ki dafa da ruwa kafin ya tafasa saiki sauke ki sirka da ruwa daidai yanda zaki iya shiga ciki ki zauna har sai ya huce kiyi kamar sau uku acikin wannan satin insha Allah zaki samu ciki idan har lafiyarki qalau saboda abinda yake kawo matsalar mace bata samun ciki shine wani lokaci maniyyin namijin ne baya samun damar shiga mahaifarta saboda wasu matsaloli misali in kofar mahaifa bata buduwa lokacin saduwarku ko karancin maniyyin namiji ajikinsa in baya fitarda shi dayawa to wayan nan abubuwan suna hana mace samun ciki to in kina amfani wayan nan magungunan mahaifa zai ringa kasan cewa koda yaushe abude kuma zaki samu ciki da yardan Allah
SIRRI NA BIYU
Kisami danyar gyada ki dakata kina shanta da ruwan zafi sau uku a rana in har kin sadu da mijinki sai kinyi ciki da yardar Allah
SIRRI NA UKU
Idan kikayi wankan haila aranar ki sadu da mijinki karki bari sai washegari don a ranar mahaifa tana kangaba nasa mun ciki
SIRRI NA HUDU
Kisami man ridi duk lokacin da zaki sadu da mijinki sai kishafa a mararki indai kikayi wannan in kinada rabon haihuwa aduniya to zaki sami ciki
SIRRI NA BIYAR
Ki sayi 🐇zomo a yanka ki gyara naman ki soya kici da bismillah ki kwanta da mijinki a ranarda kikaci naman insha Allah zakiyi ciki
SIRRI NA SHIDA
Kisami habbatus sauda ki dake shi ki hada da manshanu ki kwaba idan zaki sadu da mijinki saiki lasa da yatsanki sau uku shima kofofi zasu bude Insha Allah
SIRRI NA BAKWAI
Yawan cin danyen dankali na hausa kijuri cinsa shima
SIRRI NA TAKWAS
In zaki sadu da mijinki kiringa karanta astagafirillahil lazimil lazi la'ilaha illallahu wa atubu ilaihi zaki sami ciki kuma zaki haifi da mai albarka Insha Allah
SIRRI NA TARA
Kisami kwan agwagwa guda biyu ki soya shida man tafarnuwa dasafe zakici kafin kikarya shi zaki fara sawa acikin ki kiyi kwana biyar kinaci insha Allah, Allah zai warware miki komeye zaki samu ciki
Dan Allah yar uwa kigwada wanda kikaga zaki iyayi san nan akula aringa yawaita kusantar maigida bawai adinga shan magani Kuma ana gudun miji ba to ta ina zaki sami cikin.
ALLAH YASA A DACE AMEEN
Comments
Post a Comment