MAGANIN CIWON ZUCIYA
1. DABINON AJWAH : Shi dabinon Ajwa yana daga cikin manyan abubuwan da ake yin maganin jinya dasu tun azamanin Manzon Allah (saw).
Acikin ZAADUL MA'AD, Ibnul Qayyim ya fadi cewar Dabinon Ajwah yana maganin iwon zuciya. Harma ya kawo wani hadisin Abu Dawud (rah) Wanda acikinsa Manzon Allah (saww) da kansa yayi umurnin cewa a bama Sa'ad bn Abi Waqqas dabinon Ajwah alokacin da bashi da lafiya.
(Duk da dai Albaniy ya raunana hadisin amma Malaman hadisi da yawa sun ingantashi).
2. ZAITUN : Man zaitun yana mutukar maganin ciwon zuciya. Hakanan 'ya'yan Zaitun din. idan ana cinsu.
3. RUWAN ZOGALE: Shima yana budewa kofoffin hanyoyin jinin da suke da alaka da Zuciyar dan Adam.
4. YIN QAHO : Manzon Allah (saw) ya lissafa Qaho acikin hanyoyin samun waraka daga kowacce chuta. Don haka masu ciwukan dake da alakah da Jini ko zuciya idan suna yawan yin Qaho zasu samu lafiya ne.
5. TAFARNUWA : Ita ma tana kashe kwayoyin chutar dake haifar da Hawan jini ko Ciwon zuciya.
6. YAWAITA AMBATON ALLAH : Shima babbar hanya ce wacce ake samun waraka daga kowanne bala'i.
Ku samu dabinon Ajwah ku nikashi ya zama gari sai ku hada da garin Habbatus sauda da garin zaitun acikin ruwan zuma sannan marar lafiyan ya rika shan cokali 2 safe da rana da dare.
Man Zaitun kuma akaranta ayatul kursiyyi da ayatul ibtaal da ayatush Shifa'i acikinsa. Sannan arika sha kuma ana shafawa ajiki.
In shaa Allah wannan duk wanda kikayi zaki samu waraka...
Comments
Post a Comment