Main menu

Pages

MAGANIN LAULAYIN CIKI INSHA ALLAH






     MAGANIN LAULAYIN CIKI:


  Don ALLAH menene magani laulauyi ban iya sa komi abaki


   Laulayin ciki, abu ne wanda yake zuwa bisa yanayin halittar da Allah yayi wa matar.


Domin akwai bambanci atsakanin su kansu matan. Wata matar tafi wata shan wahala alokacin laulayin.


Ga wasu magunguna nan anema ahada. In sha Allahu za'a dace:


(1). Ganyen Na'a-Na'a (Fresh ko busashe mai kyau).

(2). Lemon tsami.

(3) Zuma mai kyau.

(4). Citta da Kanumfari._

Adafa ganyen Na'a-Na'a kamar cokali uku acikin ruwa kofi daya. Azuba citta da kanumfari daidai misali a dafasu tare.



Idan an sauke, an tache ruwan sai a zuba zuma gwargwadon yadda ake so. Sannan a yanka lemon tsami guda biyu. amatse acikin ruwan tea din sannan a sha In sha Allahu za'a samu sauki.



Mai Juna biyun zata samu qarfin jiki, zata dena yawan zubar da yawu (Miyau) da hararwa (amai) Kuma jaririn dake cikinta zai samu kaifin basira da Hankali.



Allah ya sauki dukkan masu juna biyun Musulmai Lafiya. Wadanda aka haifa kuma Allah ya raya mana su.


           Allah ta'ala Yasa mudace



        ​

Comments