HADIN GUMBA
Kunnuwan bagaruwa
Agallashe
Minannas
Kanun fari
Gero
Sugar
Zaki hada kunnuwan bagaruwarki da agallashe ki daka su sudaku sosai sai kisa matankadi ki tankade su suyi laushi sosai ki aje gefe saiki dauko kanunfarinki da minannas masu yawa zakisa sannan kidauko tuntuben halshe shima ki hada su guri daya ki dakasu su daku sosai.
Saiki tankadesu suyi laushi sosai suma ki ajiyesu gefe sannan shima geronki ki surfashi yasurfu saiki wanke idan ya bushe saiki kaishi nika maki shi, kitankade shi kicire dussa saiki samu tukunyarki ki dorata awuta saiki zuba suganki yaita dahuwa idan yadahu zaki gane idan yadahu zaita fidda kunfa sosai shine alamun yadahu
kuma zaki iya debo dan kadan a cikin cokali idan kikaga yadaskare bai dahu ba idan kuma kinkaga yana yauki to yadahu saiki hade kayanki gaba daya guri daya ki yamutsasu sai kinga sun hade sosai sannan ki zuba su achikin wannan sugan
kisa muchiya kina tukawa kina tukawa sai kinga kayan sun hade da wannan sugan sannan kisamu bokitinki mai tsafta kizuba achiki kisamu madara ko nono kina damawa kinasha himmm sister lafiya laune fa
Comments
Post a Comment