Main menu

Pages

MATAKAN DA YA KAMATA ABI WAJEN DAUKAR 'YAR AIKI 02

 





  SU WA YA KAMATA A ‘DAUKA AIKI


Mai aikin da zaki ďauka ya danganta da yanayin mijinki da gidanki. Idan mijinki bangaren sa daban babu abun da zai hada shi da me aiki, ko kuma shi ba mai zama bane to wannan da sauqi.



1. Ki sami tsohuwa mai kwari: Suna da dadin aiki, barsu dai da surutu in kin samu mai magana amma za a miki aiki. Kuma kafin ki ce a yi sun san me ya dace sai ki ga an yi. Irin wannan mijinki is safe koda suna haduwa muddin ba tada yara ‘yan mata. Domin an samu wacce ta raba auren wasu ta tura ‘yarta, wata kuma bata raba ba amma sun bi boka sun bi malam an aure mijin. Ita ma sai a san yanda za a zauna da ita.




2.Bazawara: To ita ma akan ďauke ta aiki amma su ma akwai ďan ganganci gaskiya. Ba a taru an zama ďaya ba, amma in bata wuce lokacin aure ba zata iya jan hankalin mijinki don bazawara na da farin jini. Za ki ga in za su zo aiki suna ďaukan wanka da kwalliya. Wasu tabbas mission ďinsu na neman miji ne.




3.Mai aure: Ana samun masu auren da babu take sanya su zuwa aikatau. To su ma dai da sauqi don da mijinta amma sai a kula don in kin samu mai halin bera zata rinqa debe miki kayan abinci tana kaiwa gidanta. Don na ga irin wannan da ido na.




4.Cikakkiyar Budurwa: Wannan duk ta fi su hadari. Saboda tana matakin da za ta iya ďaukan hankalin ko wane namiji. Kuma babu abun da take nema sai attention ďin namiji koda ba auren sa zata yi ba.




5.Yarinya ‘yar sha daya zuwa sha shida: Kun ga yarinya ce da zata tayaki aiki na ba a rasa ba. Kuma zaki iya in ta kusa zama budurwa sosai ki mayar da ita in kina ganin akwai matsala da mijinki. Amma suma basu da guarantee don yar shekara 8 ma sai a samu ta san namiji.




Rashin sanin yanayin mutanen da zaki ďauko su tayaki aiki akwai matsala. Sai ki duba irin macen da kika san bata burge mijinki. A misali kin san shi fara yake so sai ki kiyaye duk wata farar mai aiki. Idan shi sarkin son qirji ne da baya sai ki nemo ququma lol. Amma ďauko irin abun da kika san maigida yana so to ai kin ba kura ajiyan nama ne.



ME YASA AKE ‘DAUKAN MAI AIKI?


Akwai dalilai da dama da suke sanya mata ďaukan mai aiki daga cikin su akwai:


1.Yawan iyali: Wato gidanki kuna da yawan da mutum ďaya ba zai iya wannan aikin ba sai da mataimaki.


2.Don raino: Kin ďauketa ne don ta taya ki rainon ďanki ko ‘ya’yanki amma ba don aikin gida ba. Za ta goya miki yaro ke kuma kiyi aikin gida. Ko tana kula miki da ‘ya’ya da tarbiyyan su kina zuwa aiki ko karatu. Irin wannan sai a kula domin an samu masu aikin da suke azabtar da ‘ya’ya idan sun kebe da yaran. Ko kuma ta shiga koya musu dabi’un banza ta ‘bata miki yara.



Comments