WASU 'YAN BAYANAI DANGANE DA SARRAFA MIYA
Best spices shine iya soya miya da iya saka maggi..
Duk sauran Kamshi ne. Amma iya soya miya shine miya. Iya saka maggi shine dandano, In mai yayi kadan a miya to zai bata taste, Idan yayi yawa zai lallata miya
Tafarnuwa
Curry
Black paper
Gyadar miya
Duk kamshi sukeyi.
Ai wacce ta kona miya sai dai tsautsayi, Indai kinaso ki soya miya ta soyu to ki rage wutar girkin, Kuma indai kinaso ki soya miya tayi kyau, To kada kiyi nisa da ita, Ya kasance kina kusa da'ita kina juyawa, Indai kinaso ki soya miya tayi kyau to ki kula gurin saka maggi, Domin in miya ta soyu maggi yana fitowa sosai, Idan kika cika tun afar kon miyar idan ta soyu zai fito daga karshe yayi yawa, Shiyasa mutane da yawa suka tafi akan cewa kasaka maggi idan ka gama soya miya yafi idan kafara..
Idan markade yayi kauri zaki dan kara ruwa ne sai ki rage wuta ki dora shi idan ya dawu sai ki zuba mai kiyita juyawa zakiga yanata kyau yana kuma kara ja, Idan kinaso miyar ki ta soyu to ya kasance da ta soyu ki kasheta kada ki barta ta soyu soyuwar da zatayi dace ko rashin dadi, Ki kuma sani indai miya ta soyu ba ruwanki da wani abu wai shi fridge, Bakya fargabar lallacewarta...
- Maggi na lallata miya..
- Tattasai na lallata miya
- Tumatur na lallata...
- Kanwa na lallata miya..
- Baking powder na lallata miya..
- Attaruhu na lallata miya..
- Gishiri na lallata miya...
- Tafarnuwa na lallata miya...
- Gyadar miya na lallata miya..
- Curry na lallata miya...
- Farin maggi na lallata miya...
-Sugar na lallata miya...
- Haka kuma daddawa na lallata miya....
- Spices na lallata miya..
Amma fa sai idan sunyi yawa indai kika cika su sukayi yawa har suka fito adandano suka fara kama baki to lallai sun lallata miki miya!!!
Amma indai kika kula gurin saka su to zasu gyara miki miyar ki ta zama abun sha'awa abin kamshi abun dadin dandano.
Yana da kyau ka lura da lokacin zuba maggi acikin miya da kuma danbum nama domin abubuwa ne da idan suka soyu suk'an fito da dandanon sa
Indai har kina sa maggi afarkon miyar ki to kinasa kadan idan ta soyu sai ki kara in baiji ba....
In kuma sai ta soyu kike sakawa to sai ki bari kifara saka daya idan yayi sai ki barshi in baiyi ba sai kikara
Domin garaje akowanne abu da nuna isa yakansa kasamu ba yadda kakeso ba....
- Miyar kuka batason kayan miya da yawa.
- In bakida nama yanka albasar ki sirisiri kisaka acikin miyar ki.
- Idan bakida nama yanka dankali kanana ki dafa ki watsa a miyar ki..
- Idan bakida agushi mitsika awara danya ki watsa acikin miyar...
- Idan bakida attaruhu daka barkono biyu ki watsa inke mai cin yaji ce...
- Idan bakida albasa kuma zaki watsa a miyar kokuma zaki soya kwai jajjaga tafarnuwa ki watsa...
- Wanda basuda zogale kuma suna son yin dambu to ku yanka alayyahu ku watsa..
- Wacce batada da alayyahu kuma tana son yin miyar taushe watsa zogale aciki....
- Wacce abincin ta yayi yaji ko markadanta watsa manja ki soya dashi..
- Wacce batada agushi kuma tanason cin miyar agushi to ki fari gyadar ki d'anya tayi fari ki daka ki watsa cikin miyar...
- Wacce miyar kubewarta take tsinke wa sai ta daina cika mata wuta..
- Wacce gishiri yayi yawa acikin miyar ta ta sauke ta jajjaga tumatur ta watsa zai ragu...
- Wacce batada kayan miya kuma ta son cin abinci mai dan dadi sai ta yanka albasar ta kanana ta jajjaga attaruhun ta in tanada zogale ko dankali ta yanka shi kanana ta watsa tasa atukunya ta zuba ruwa madaidaici su dawu sai tasa mai da maggi tasa attaruhun ta in sunyi sai ta sauke...
Allah ubangiji ya hadamu a ladan baki dayan mu...
Comments
Post a Comment