HAIHUWA A SAUKAKE
RAGE YAWAN LAULAYI:- Babu wani magani dayake hana laulayi gabaɗaya face sai dai asami sauƙin hakan. Da Farko za'a sami bakin zobo, kanumfari, garin Citta kaɗan, Habbatussauda, Sai a tafasasu, atace ruwan sai asa Zuma, ta rinka sha kaɗan kaɗan..... Wannan zai rage mata yawan kasala da amai.
GA MACEN DA TAKE YAWAN JIN TASHIN ZUCIYA BAYAN TACI ABINCI :- Ta sami Citta kaɗan ɗanya, saita rinka ɗan taunawa tana tsotse ruwan. InshaAllah wannan zai kashemata wannan tashin zuciyar.
YAYIN DA CIKIN MACE YAKAI WATA 3 KO 4:- Anaso ta yawaita cin Ayaba. Sannan ta kiyaye waɗannan abubuwan::-
1. Ta daina zama kanta babu ɗankwali ko hula, domin kuwa alokacinne shaiɗanun Aljanu ke barazanar shiga jikinta, donsu cutar da abinda ke cikinta.
2. Ta daina zama a tsakar gida jikinta abuɗe.
3. Ta daina zama aiki goshin magariba, duk abinda take da zarar ankira sallar magariba ta dakatar koda kuwa lokacin bata Sallah ne, duk da zaiyi wuya kasami irin hakan, Amma akwai wasu matan masu irin hakan. To saita bari bayan magariba sai tacigaba da aikinta.
4. Ta kiyayi kallon kaɗe-kaɗe, raye-raye da waƙoƙin zamani.
5. Ta kiyayi wasannin banza da irin raye-rayen zamani da wasu abubuwan da matan banza sukeyi.
6. Ta rinka tsabtace jikinta da ɗakin da take, tanasa karatun Al-Qur'ani mai girma.
7. Ta cire hotunan dake liƙe/rataye/kafe acikin ɗakinta.
LOKACIN DA CIKIN MACE YAKAI WATA 6::- Anaso tayi amfani da Lubazzakar, Kanunfari, Na'a-Na'a, da Ganyen Zaitun, ta rinka tafasasu tanasha ;sukansu malaman tsubbu cewa sukai matar data saba shan waɗannan abubuwan a cikinta da ɗanta, to Insha Allah zata haifi yaro/yarinya ya zama haziƙi, Sannan ita kanta zai amfaneta, kuma shannasu zai zamto yana wankemata zakin jikinta, ɗan da zata haifa zaizo lafiya. Ƙalau.
LOKACIN DA CIKIN MACE YAKAI WATA 7 KO WATA 9 (Duk ana iya haihuwa).
ABUBUWAN DAYA KAMATA ATANADA KUSA DA ITA SUNE:::-Zam Zam, Hijiratul Maryam wanda akafi sani da(HANNO), Dabino, Raihan wato (ƊAƊƊOYA) Suna da matukar muhimmanci. Kuma suna taimakawa wajen samin sauƙin haihuwa.
Akwai matar da take naƙuda 1week, wata 5days, wata kuma tana daukar tsawon lokaci, Abinda akafiso a al'adunmu na hausa, shine mace ta haihu da kanta, amma da yawa Turawa ko Larabawa sai asami mace tai haihuwa 10 amma duka dazarar ta fara naƙuda sai akaita asibiti amata CS aciro ɗan. Su hakan al'adarsuce.
ALOKACIN DA MACE TA FARA NAKUDA AKWAI WASU ADDU'OI DAYAKAMATA TARIƘAYI(inzata iya) DA KUMA MAGUNGUNAN DA MUSULUNCI YACE TAYI AMFANI DASU KAMAR HAKA.
ƁANGARAN ADDU'OI ::-Kisami Zam-Zam, sai asami kwano mai tsafta ajuye ruwan aciki, Sai a karanta waɗannan ayoyi masu zuwa ƙafa bakwai-bakwai(7)
1. Ayar ƙarshe ta cikin 'Suratul Yusuf' wato:(LAQAD KANA FIIQASASIHIM IBRATUN LI'ULEE ALALBABI MA KANA HADEETHAN YUFTARA WA LAKIN TASDEEQA ALLATHEE BAYNA YADAYHI WATAFSEELAKULLI SHAY'IN WA HUDAN WARAHMATAN LIQAWMIN YAWMIN NUNA(7) Sannan za'a karanta
2.Ayar karshe ta cikin SURATUL AHQAf. Afara daga KA ANNAHUM.. HAR ƘARSHENTA Wato ::-(KA ANNAHUM YAWMA YA RAWNAMAA YU'ADUNA LAM YALBATHU ILLASSA'ATAN MINNAHARIN BALAGHUN FA HAL YUHLAKU ILLA ALQAWMU ALFASIQUUN. kafa(7).
3. Ayar ƙarshe ta cikin SURATUL NAZI'AT wato(KA'ANNAHUM YAWMA YARAWNAHA LAM YALBATHUU ILLA'ASHIYATAN AWDUHAHA. kafa(7).
Sanna inzata iya lokacin da tafara jin nakudar tayi ALWALA, sannan inzata iya saita rinka karanta wannan addu'ar:- ALLAHUMMA LAASSAHALA ILLAMA JA'ALTAHU SAHALA WA'ANTA, TAJ'ALUL HAZNU IZAH SAHALA.
ƁANGARAN MAGANI::- Asami HIJIRATUL MARYAM (Hannu) a jikashi aruwa minti kaɗan inyayi sai abata tasha.
Sannan ana amfani da RAIHAN(Ɗaɗɗoya) itama jiƙata akeyi sai asha. Dukkan waɗannan abubuwan suna taimakawa sosai.
""Kuma InshaAllah yanda kikasan zare gashi acikin mai haka zata haihu lafiya".
BAYAN MACE TA HAIHU:-
1. Wata tana samin matsalar ɓallewar jini, to ta sami DABINO mai bauri, wannan sunnace mai ƙarfi tunda NANA MARYAM tayi amfani dashi. Saiki sami DABINO mai bauri saikici, jini bazai ballemikiba InshaAllah. Ko kuma ki sami NONON RAQUMI kisha, jini bazai ɓallemikiba InshaAllah.
2. Wata tana samin irin kumburin cikinnan, saikaga cikinta ya girma sosai, :Tota sami NA'A-NA'A da KANUNFARI saita tafasa tasaha. Wannan zai hana miki wannan kumburin cikin.
MIJINKI BAYANAN KIN HAIHU YAZAKI:! Kina haihuwa aka yankewa yaro/yarinya cibiya aka mai wanka, abinda yakamata kiyi shine::Ki daukeshi da kanki, ki abinda Manzon Allah (SAW) yayi lokacin da NANA FAƊIMA wato Ɗiyar annabinmu Muh'd (SAW) saiya umarci su NANA ZAINAB dasu ɗaukoshi, bayan an miƙo masa jaririn saiya karantamasa AYATUL QURSIYYU, Ya kuma karantamasa AYata 54 acikin SURATUL AL-ARAF wato(INNA RABBUKUMULLAHULLAZII KALAQASSAMAWATII WAL ARDI FII SITTATI AYYAMI THUMMASTAWA ALAL ARSHI........... har izuwa ƙarshen ayar.
Idan bazaki'iyaba ki karanta AYATUL QURSIYYU kawai
2.saikimai kiran sallah akunnensa na dama
3. Tada Hiƙama akunnensa na hagu... Amma awata ruwayar ance kiran sallah kawai yaymasa akunnensa na dama, wata ruwayar kuma ance Annabinmu (SAW) yayimasa akunnensa na dama dakuma na hagun. Wallah a'alamu.
4. Saiki ambaci sunansa kice Sunanka...... Misali kice Sunanka Muhammad basai ranar sunaba, saiki tauna DABINO saikiɗan buɗe bakinsa saikisamai, abinda akafiso kenan yaro yafaraci arayuwarsa kenan, sannan sai ki samasa Albarka. Sannan kullum kirinƙa yiwa ɗanki addu'oin kariya. Wato kice U IZUKUMA BI KALMATILLAHI TAMMAT, MIN KULLI SHAIƊANUN WA HAMMAH, WA KULLI AYNIN LAMMAH. Saiki tofa ki safe jikin ɗanki dashi.
Comments
Post a Comment