DAHUWAR KAZAR AMARYA
A kasar hausa an samo dafa kazar amarya tun shekaru da yawa da suka wuce wanda kabilar hausa da kanuri keyinta amatsayin al'adar biki, a wannan lokacin kowacce amarya nada uwar dakinta bayan mahaifiya, wannan uwar dakin ita take dafa kazar saidai awannan lokacin babu tunanin wani magani da akeyi sai a shekarun baya wanda akallah sama da shekara 20 aka fahimci hada wannan kazar a zamanance don tayi amfani ga amarya.
Har yanzu babu wani bincike da bayanin dafa kaza yake dashi wanda za'ace ansamu daga wani marubuci, shi dai abune da kowa yana iya kirkirarsa matukar yanada sani akan harkar maganin mata wanda hakan yasa na tattaro bayanai akan yanda ake dafawa ta hanyar amfani da ganye da itatuwa wanda ko kadan be sabawa shari'a ba.
Hanyoyin dafa kazar amarya suna da yawa amma yakamata mu duba abinda mutane sukafi saninsu,
kayan hadi guda 30 da wanda sune kan gaba wajen dafa kaza.
1 Minanas
2 Kanunfari
3 Ridi
4 Biya rana
5 Dan kadafi
6 Malmo
7 Gadalin mata
8 Habbaba
9 Nonon rakumi
10 Nonon akuya
11 Dan kumasa
12 'Ya'yan baure
13 Sassaken baure
14 Geron mata
15 Dan bashanana
16 Citta me yatsu
17 Man ayu
18 Gishirin gallo
19 Manta uwa
20 Kukuki
21 Habbatus-Sauda
22 Garin Raihan
23 Cokali hudu
24 'Ya’yan Zogale
25 Kabewa
26 kirfat
27 'Ya'yan kankana
28 Ganyen mallaka
29 Farar albasa
30 Bawon biya rana
A yanzu zan jero bayanine akan yanda ake dafa kazar amarya wato hanyoyi shida wanda kadanne daga cikin binciken da a kayi wanda koda daya kikayi keda kanki zakiji alamar kinci kaza don kuwa yana ciko da gaban mace ya kara mata ni,ima wasu har mallakar miji suke da wannan kazar nishadi lokacin saduwa kuwa kullum kamar amarya zaki zama.
1. zaki gyara kaza budurwa amma kada ki fedeta yanda zakiyi ta kasanta zaki ciro hanjin da kai da kafa, to saiki dafa da ruwa zallah sama sama saiki sauke dama kuma kin daka dan kumasa da kanunfari da minanas da ridi da habbasusauda saiki hada wannan garin waje daya sannan ki dauko kayan kamshinki
Irinsu tumatir da albasa dasu karas saiki hada da wannan garin duka ki zuba cikin wannan kazar wato inda kika ciro hanjin,
shikenan sai nonon rakumi shine ruwan dafawa shikenan ki dora akan wuta ta dafu sosai saiki sauke ki cinye gaba daya.
Comments
Post a Comment