HANYOYI GOMA (10) WANDA ZA A BI DON GYARA..
1; Idan ana so a gyara gashi za a iya hada ayaba da kwai sai a kwaba su sosai sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar (15) zuwa talatin (30) sannan a wanke.
2: - Domin gyara farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar (5) sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi matukar kyau sosai.
3: Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai santsi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar (15) zuwa ashirin (20) sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya ma a sati za a ga canji.
4: Ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke makale a gefen gashin kai.
5: Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rika shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka bakin da ya bayyana a wasu gabbai ko sassan fata.
6: Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rika dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.
7: Man kwa-kwa na matukar gyaran zubewar gashin ka. Za a iya shafa man kwa-kwa a fatar ka, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.
8: Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwa-kwa.
9: A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai. Sannan a rika shafawa a kan kurajen fuska. Yin hakan na kashe su sosai.
10: Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata.
Comments
Post a Comment