Main menu

Pages

MIJIN ALJANA YA 'BARA YA FADI GASKIYAR AL'AMARI



 "Wallahi Karya nike kawai Na fada ne don na samu na abinci" Cewar Mijin Aljana.


A kwanakin nan ne wani mutum mai Suna Ahmad dake siyar da maganin gargajiya ya bayyana a kano, Inda Malam Ahmad yace shifa da ake gani yana da Mata Aljana harma ta haifa masa yara shida.



Ya dauko tarihi Inda yace tun yana qarami mahaifiyarshi ta fada rijiya dashi a vote, to daga nan ne fa a cewarshi sai sarkin aljanu ya dauke shi ya tafi dashi can.



A can ya girma har ya auri aljanar da ta haifa mashi yara shida. Bayan nan kuma ana biyanshi tana bugs ma mutane kudi.


To fa jin wannan yasa Gwanatin kano a karkashin Ministry of religious affairs suka hada mukabala don zama da wannan Mijin Aljana don jin yadda batun yake dalla dalla, wanda har matar Mijin Aljana tace duk abinda ya fada gaskiya ne.



To bayan zama dai an kure Ahmad Mijin Aljana, Inda da bakinsa yace shifa duk abubuwan da yake fada karyane kawai yayi hakane don ya samu cinikin maganin gargajiya da yake siyarwa, ya kara dacewa shi fa kawai yayi ne don ya samu kudi yaga ya girke buhun shinkafa da na dawa.



Sannan a nan take ya nemi a bashi dama ya nuna yadda yake damfarar mutane wajen buga masu kudi, Inda yake amfani da wata takarda mai rubi biyu gaba da baya, sai ya saka kudi a cikin daya gefen sai ya nude daya gefen kuma ba komai ciki to nan yake zuba garin magani yayi surutai irin na surkulle, sai yasaka cikin littafi yayi ta surutan.


Mutane hankalinsu naga surutan da yake sai ya juya littafin hannunsa sama ya koma qasa, da an bude sai a ga kudin da yasa a kasan. Don haka sai mu kiyaye ire item wadan nan mutane sake damfarar mutane.



Ya nemi afuwar kowa da kowa ya kuma nemawa matarshi afuwan karyar shedar sure din da tayi.


To muma rokon Allah Ya tsaremu daga irin wadannan mutane, Ya shiryesu in masu shiryuwane.

.

Comments